ZABE: Za ayi amfani da masu yi wa kasa hidima 5,500 a Sokoto

0

Jami’in hukumar NYSC na jihar Sokoto Philip Enaberue ya bayyana cewa INEC ta horas da masu yi wa kasa hidima 5,500 a matsayin ma’aikatan wucin gadi na zaben da za ayi ranar Asabar a jihar.

Enaberue ya fadi haka ne a taron kara jadadda gudanar da aiki bisa ga sharrudda da dokokin hukumar zabe, INEC wanda hukumar NYSC ta shirya ranar Juma’a a garin Sokoto.

” NYSC na kira a gare ku da kada ku yadda wani yayi muku dadin baki ko kuma abin duniya ya rude ku ku bujirewa yin aikin ku yadda ya kamata a lokacin zabe.

Enaberue yace NYSC za ta hukunta duk wadanda suka karya doka.

Ya kuma shaida wa masu yi wa kasa hidiman cewa jami’an tsaro sun kammala shiri tsaf domin ganin sun kare rayukan mutane a lokacin zabe.

Idan ba a manta ba jami’ar hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Zamfara Asma’u Maikudi ta sanar was manema Labarai cewa hukumar ta horas da ma’aikatan wucin gadi 15,577 da za su yi aikin zabe a jihar.

Asma’u ta ce ma’aikatan sun hada da daliban jami’o’I, masu yi wa kasa hidima da dai sauran su sannan za su shugabanci wasu fanonni a rumfunan zabe a dalilin horan da suka samu kan aiyukkan zabe.

Sannan a kwanakin baya ne Kwamishiniyar Zabe dake Kula da shiyyar Kaduna, Anthonia Sinbene ta bayyana cewa hukumar za ta horas da ma’aikatan wucin gadi 35,000 aiyukkan zaben da za a yi a watannin Faburairu da Maris.

Sinbene ta ce wadannan mutanen da za su horas za su shugabanci wasu fannonin aiyukkan zabe a rumfunar zabe 5,102 dake kananan hukumomin jihar. Sannan sun zabo su ne daga cikin wadanda suka nemi aikin.

Share.

game da Author