Mataimaki Babban Darektan hukumar NSCDC Kelechi Madu ya bayyana cewa za a yi amfani da jami’an taro na NSCDC 60,000 domin samar da taro a duk fadin kasar nan a zaben da za ayi ranar Asabar.
Madu ya fadi haka ne da yake zantawa da wakilan Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
Ya ce NSCDC ta raba jami’anta zuwa jihohin kasar nan da babban birnin tarayya, Abuja domin samar da tsaro tare da hadin guiwar sauran hukumomin tsaro na jihohin kasar nan.
Madu ya ce a Abuja hukumar ta saka jami’an ta a wurare daban-daban sannan wasunsu an basu bindigogi.
” Ma’aikatan mu da muka saka a Abuja basu da damar amfani da makaman da ke hannun su duk iya rikicin da mutum zai tada a gaban su amma za su iya kama su domin danka su hannun ‘yan sanda domin a hukunta su.
” Ina kuma so in gargaddi dukka ma’aikatan mu cewa hukumar za ta hukunta duk ma’aikacin da ya yi amfani da makaminsa a mutane.
A karshe Madu ya yi kira ga mutane da su nisanta kansu daga duk abin da zai tada rikici a lokacin Zabe.