Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya gana da wasu shugabannin jam’iyyun siyasa da shugabannin hukumomin tsaro a jihar Ogun.
An yi ganawar ce jiya Asabar a Dakin Karatu na Obasanjo, da ke cikin katafariyar gonar sa, a Otta, jihar Ogun.
Jam’iyyu hudu ne suka halarci ganawar, wadda aka yi domin tabbatar da cewa an gudanar da zabe lami lafiya a jihar.
Akwai jam’iyyar APC, APM, ADP da ADC.
A bangaren jami’an tsaro kuwa, wadanda suka halarta sun hada da sojoji, ‘yan sanda, DSS da NSCDC.
Shugaban Jam’iyyar ADP, Wale Ogunleti, ya bayyana wa manema labarai bayan kammala taron cewa sun cimma matsaya daya ce domin tabbatar da cewa an kauce wa tashe-tashen hankula a jihar, kafin zabe, lokacin zabe da kuma bayan kammala zabe.
“Kun san an san jihar Ogun da son zaman lafiya. Shi ne ya sa dattijon ya kira mu domin ja mana kunne da kuma shawarwarin tabbatar da dorewar zaman lafiya a Ogun.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ya ruwaito cewa wani yamutsi da wasu magoya bayan jam’iyyun siyasa biyu a jihar suka gwabza, har aka ji wa wasu raunuka, aka kuma lalata dukiya.
Hakan shine ya sa dattijon ya Kira taron jami’an tsaro dake Jihar da su zo a tattauna yadda za a gujewa tashiwar irin haka a Jihar.