Jami’in hukumar kula da aiyukkan zabe na jihar Adamawa (INEC) Kasim Gaidam ya bayyana cewa mata 52 suka fito takarar kujeru daban daban a zaben 2019 a jihar.
Gaidam ya fadi haka ne a taron wayar da kan wadannan mata da suka fito takara game da zabuka da aka yi a Yola ranar Alhamis.
” Mata biyar sun fito takar kujeran gwamna, bakwai na takarar kujeru daban daban a majalisar dattawa, 11 sun fito takarar kujerun majalisar tarayya sannan 21 na takarar kujerun majalisar dokoki na jihar.
Gaidam ya ce shiga ciki al’amuran siyasa da mata suka yi ya nuna irin ci gaban da dimokradiyya a Najeriya ta yi.
Ya kuma yi kira ga mata da kada su shashantar da ‘yan cin su na yin zabe da suke da shi.
A karshe jami’in kungiya mai zaman kanta ‘Life Helpers Initiative’ Tayo Fatinikum ya ce INEC ta shirya wannan taro ne domin wayar da kan mata game da harkokin zabe sannan da mahimmiyar rawar da za su iya takawa wajen ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali.