ZABE: Hanyoyi 7 da zaka kada kuri’ar ka ba tare da samun cikas ba

0

Akalla mutane miliyan 84 ne za su fito domin kada kuri’un su a zaben shugaban kasa, gwamnoni,’yan majalisar dokoki na kasa da na jihohi da za a yi ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu.

A dalilin haka ne Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) ta bayyana hanyoyi 7 da za su taimaka wa masu zabe wajen kada kuri’un su ba tare da matsala ba.

Ga hanyoyin:

1. Tantance masu zabe zai fara ne da karfe takwas na safe zuwa biyu na rana a runfunar zabe. Kowa ya zo zai shiga layi ne.

2. Idan an zo kan ka ma’aikacin INEC zai karbi ainihin katin zaben mutum domin tattance ta da na’uaran tattance katin zabe.

3. Idan na’urar ta tabbatar cewa mai zabe na rumfar zaben da ya kamata ma’aikacin INEC zai maka shaida haka da alkalami a yatsar ka.

4. Daga nan ma’aikacin INEC zai saka hannu a duk takardun zabe kafin a raba wa masu zabe.

5. Da zaran mutum ya karbi takardar sai ya dangwala yatsarsa a ruwan alkalami sannan ya dangwala wa hotan jam’iyyar ad yake so dake kan takardar zabe.

6. Mai zabe zai lankwasa wannan takarda a baibai ko kuma ta waje domin hana wannan ruwan alkalamin taba wani wuri a takardar zabe.

7. Sai ya jefa takardan a akwatin zabe inda daga nan mutum zai tafi gidan sa ko kuma ya nemi inuwa ya zauna domin jiran a fara irge.

Share.

game da Author