ZABE: ECOWAS ta turo masu sa-ido 200

0

Kungiyar Cigaban Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, ta turo wakilan sa-ido kan zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya har mutum 200.

Kwamishinan ECOWAS mai lura da lamurran siyasa, zaman lafiya da sha’anin tsaro, Francis Bejanzin ne ya bayyana haka a Abuja.

Ya ce tawagar ta na karkashin tsohuwar shugabar kasar Liberiya, Elen Johnson Sirleaf.

Ya ce dama tun a cikin watan Disamba, 2018 sai da tawagar mutane biyar ta zo ta gana da INEC da sauran hukumomin da zabe ya shafa, inda su ka ga irin shirin da Najeriya ta yi wa zaben.

Ya ce daga baya an sake turo wata tawaga ta jami’ai 27 da za ta ci gaba da aikin lura da yadda sha’anin zaben ke gudana.

A yanzu dai ya ce tawagar ta kunshi jami’ai 200, wadanda za su sa-ido wajen zabe, kuma bayan kammala zabe za su bayyana rahoton su domin a yi nazarin yadda ya gudana.

A na ta bangare, Elen ta ce ECOWAS ta zo ne domin a ta taimaka a gina ingantacciyar hanyar zabe, wadda za ta zama abin koyi a wannan yanki na Afrika ta Yamma baki daya.

Ta ce sakamakon da za su fitar, zai kasance wani ma’aunin da za a yi wa sahihancin zaben alkalanci.

Sai dai kuma ta ce ‘yan Najeriya ne da kan su ke da alhakin gudanar da zaben su a cikin lumata da kwanciyar hankali.

Share.

game da Author