A yau Asabar da karfe 8:05 na safe Shugaban kasa da uwargidan sa Aisha suka lada kuri’ar su a rumfar zabe na 003 dake Daura.
A wurin zaben, Buhari sai da ya yi wa matar sa Aisha raha, cewa bayan ya jefa kuri’ar sa ya dan leka na Aisha ne domin itama ‘yar Adamawa ce kuma babban Abokin hamayyar sa dan Adamawa ne.
Idan ba a manta ba a jiya Juma’a ne jirgin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dira a garin Katsina ranar Juma’a da rana.
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari da wasu Sanatoci ne suka tarbe sa a filin jirgi na Katsina Inda bayan ‘yar kwarya-kwaryar maraba da aka yi masa sai ya zarce garin Daura.