ZABE: Bi mu kai Tsaye a nan

0

A yau ne miliyoyin ’yan Najeriya za su jefa kuri’un zaben shugaban kasa, wanda zai shugabanci kasar da ta fi kowce kasa yawan jam’a a Afrika ta Yamma, kuma kasar da ta fi sauran kasashen bakar fata na duniya yawan jama’a, watau Najeriya.

Duk a yau ne kuma za a zabi ’yan Majalisar Tarayya 468, wadanda suka kunshi na Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Sannan akwai masu takarar shugabancin kasa har 73, amma dai hankulan kowa a kasar da ma duniya baki daya, sun karkata ne a kan manyan ‘yan takara biyu, Muhammadu Buhari, wanda shi ke kan mulki kuma mai wakilar jam’iyyar APC da kuma Atiku Abubakar mai waklitar jam’iyyar PDP.

Buhari ne ya kayar da shugaban kasa da ke kan mulki, a zaben 2015, watau Goodluck Jonathan, da ratar kuri’u sama da milyan biyu. Ya maida hankali kan manufofi uku a kan mulkin sa, watau kashe cin hanci da rashawa, magance matsalar tsaro da kuma inganta tattalin arziki.

Duk da Buhari ya samu kalubale a wadannan fannoni uku, shi da magoya bayan sa na bugun kirjin cewa sun yi rawar gani, kuma sun cancanci a sake zaben su tsawon wadansu shekaru hudu.

Tun bayan da Atiku ya bar mulki a matsayin mataimakin shugaban kasa cikin 2007, sau uku ya na jaraba neman shugabancin kasa. Ya fito takara a 2007, cikin 2011 da 2015 kuma tun a zaben fidda-gwani aka kayar da shi.

Manyan manufofin da Atiku ke tinkahan alkawarin aiwatarwa idan ya samu nasara, sun hada da samar da aikin yi ga matasa, inganta tattalin arziki da kuma sake fasalin kasa.

Kuma ya na bugun kirjin cewa Buhari ya kasa duka abin da aka zabe shi domin ya yi. Don haka a yanzu shi ne mafita ga ‘yan Najeriya.

’Yan takara 1,094 ne ke neman kujerun sanata 109, yayin da masu takara 4,680 ke neman kujerun majalisar tarayya 360.

Mutane miliyan 72,775,585 ne suka yi rajistar kada kuri’a a yau Asabar da kuma zaben gwamna mai zuwa nan da makonni biyu. Jihohin Lagos, Kano, Kaduna, Katsina da Rivers ne masu yawan kuri’u fiye da sauran jihohin kasar nan.

Za a jefa kuri’a a runfunan mazabu 57,023 a rumfunan zabe 119,023.

PREMIUM TIMES HAUSA za ta rika kawo muku yadda zabe ke gudanar a dukkan fadin kasar nan, kai-tsaye. Sai a rika bin mu daki-daki.

INEC ta ce za a fara zabe karfe 8 na safe.

A jihohi da dama na kasar nan tantance masu Zabe yana gudana yadda kamata.

SAFIYAR ASABAR

Mutane sun yi tururuwa zuwa rumfunar Zabe domin a tantance su. Zuwa yanzu dai rahotannin daga jihohin Legas, Kaduna, Kano, Ogun, komai na tafiya yadda ya kamata.

Shugaba Muhammadu Buhari da Uwargidan sa duk sun kada kuri’un su a garin Daura.

Jihar Barno

Garin Maiduguri ya tashi cikin rudani a safiyar ranar Zabe inda Bama-bamai har 11 suka tashi a garin.

Wani dan sanda ya tabbatar da haka wa PREMIUM TIMES.

Bayan haka a wata majiyar kuma ta tabbatar cewa BokoHaram ta kai wa garin Gaidam dake jihar Yobe hari ranar Asabar.

Majiyar ta bayyana cewa Boko Haram sun kai wa garin hari ne da karfe uku na asuba.

Wata mazauniyyar garin Potiskum Fati Umar ta bayyana wa wakilin mu cewa tun daga wannan lokaci suka rika jin karan harsashin bindiga.

Bayan haka jiya da yamma wasu ‘yan kunan bakin wake na Boko Haram sun kai wa kauyen Zabarmari hari.

Kauyen Zabarmari kauye ce dake kusa da Jere da Maiduguri a jihar Barno.

ABUJA

Wakilinmu da ya kewaya har Mazabar Ushafa da ke cikin Karamar Hukumar mUlki ta Bwari, ya ci karo da wata mata mai suna Rosemarry, wadda ta rika bambami ta hayaniya cewa INEC ta zalunce ta.

“Na yi ta zirga-zirga zuwa ofishin INEC domin karbar katin rajista na, amma sai su ce min babu kati mai suna na. To yanzu ga shi na zo wurin zabe, kuma ga suna na nan a cikin rajista na gani. Inji Rose Marry.

SOKOTO

Duk da cewa Doka Zabe ta hana a je wurin jefa kuri’a da duk alama da aa ta nuna tallar dan takara, amma a Mazabar Hakimi ta Karamar Hukumar Wammako, wakilin mu ya ga an lika fastocin tallar Sanata Aliyu Wammako.

Duk da wasu tsagerun matasa sun tare fastar, ba su son jama’a su gani, amma sai da wakilin mu ya yi tamaza ya kutsa ya gane wa idon sa.
Mazabar da APC ce ke da fifikon magoya baya. Shi ya sa ma a wani gini a tsallaken inda aka lika fastar, an yi wani babban rubutu a jikin wani gida, aka rubuta “Ali Ya Gode.”

KANO

A wata mazaba ta Kadawa, wakilin mu ya ci karo da Jami’in Zabe na yankin ya na korafin cewa Na’urar tantance Katin Zabe ta kasa tantancewa, sannnan kuma babu SPO ballantana a nemi mafitar yadda za a magance matsalar.

EDO

A wata runfar zabe da ke cikin Firamare ta St. John, an raba musu takardun jefa kuri’a 600, maimakon 647 adadin da suka yi rajista a yankin.

Sun yi magana an ce ai ba ma za su iya cike dukkan adadin da aka ba su ta 600 din ba.

Yadda sojoji suka tare hanyar da Osinbajo zai wuce ya jefa kuri’a

An nemi jami’an aikin zabe na wucin gadi da aka tura aikin zabe a mazabar Mataimakinn Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.

Har zuwa karfe 8:07 na dare, babbu wani jami’in zabe a rumfar zabe ta VGC PU2 a Lagos.

Sai wani jami’in dan sanda daya mai suna Geoffrey ne kadai aka gani ya na ta kewayen wurin.

Sai dai kuma komai ya kasance a tsare, an jera kujeru da teburan dora kayan zabe. Kuma akwai jama’a akalla 100, a zaune sun a jiran a fara kada kuri’a.

ARTABUN OSINBAJO DA WASU SOJOJI

Wasu sojoji da suka datse hanya su ka hana jama;a wucewa, sun kuma hana tawagar Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo da ta Gwamnan Jihar Lagos wucewa.

Sun datse hanyar da ta tashi daga Toll Gate zuwa VGC, kuma suka ce umarni ne aka ba su, kada wanda aka bari ya bi ya wuce. Sojojin na rundunar B1 ne.

Jami’an sojojin sun ce an ba su umarni ne kada a bar kowa ya bi ta hanyar, tun daga 6 na safe zuwa 6 na yamma.

Sai da aka shafe mintina 20 ana ja-in-ja, sannan aka ga ‘yan sandan mobal sun fito sun cire shingayen kan titi domin Osinbajo shi da tawagar gwamna ta samu wucewa.

Rikici ya barke a jihar Ebonyi

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ebonyi Awosola Awotunde ya bayyana wa PREMIUMTIMES cewa rikici ya barke a mazaba ta daya a kauyen Amagu dake karamar hukumar Ikwo a jihar.

Awotunde ya ce a dalilin wannan rikicin mutane biyu sun mutum sannan da dama sun sami rauni.

Ya ce magoya bayan jam’iyyu biyu ne suka gwabza.

RIBAS

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ribas Omoni Nnamdi ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an harbe mutane hudu a lokacin zabe a karamar hukumar Andoni.

Kakakin jam’iyyar APC a jihar Senibo Finebone ya bayyana cewa wasu tsageran jam’iyyar PDP sun harbe wani jigon jam’iyyar APC Mowan Etete.

Finebone ya kuma kara da cewa tsageran sun kuma bindige wasu ‘yan uwan sa biyu sannan da wani jami’in jam’iyyar APC mai suna Ignatius.

” Duk wannan abin tashin hankalin ya faru ne a karamar hukumar shugaban jam’iyyar PDP Prince Uche Secondus wato Andoni.”

Nnamdi ya ce rundunar ta dauki matakan samar da zaman lafiya a karamar hukumar sannan har sun fara gudanar da bincike domin kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Kafin ranar zabe rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa ta kammala shiri tsaf domin ganin ta hana tashin hankali da rikici da aka saba samu a jihar a duk lokacin zabe.

OYO
A Mazabar Isale da ke garin Oyo, a jihar Oyo, wadanda suka yi sammako domin zuwa jefa kuri’a sunn tayar da hayaniya. Wakilin mu ya luda da yamutsi ya kai ga har akwatin zaben da aka sani a gaban layin masu kada kuri’a, ya koma can bayan jama’a.
Ya kuma ga yadda wasu jami’an ‘yan sanda biyu, mace da namiji ke ta kokarin kwantar wa jama’a hankali, su na gaganiyar maida jama’a su hakura su daina gargitsi.

FILATO

Wakilin PREMIUM TIMES ya lura da cewa a mazabu da rumfunan zabe da dam aba a fara jefa kuri’a da wuri ba. Har zuwa 9:45 ba a kai kayan zabe a wurare da dama ba. Wannan ya bata wa dama daga cikin su rai, domin kowa ya fito tun da wuri da niyyar yin zabe.

ANAMBRA: MATSALA A AKWATIN RUMFAR PETER OBI

Daidai karfe 9:06bna safe a Mazabar Agulu ta Anaocha, an samu mishkilar baddala akwatinan zabe.

An ci karo da matsala yayin da a Mazabar Peter Obi, dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, an dora bakin murfi a kan akwatin jefa kuri’a na shugaban kasa.

EDO

A Mazabar Ughiogwa ta 1, a garin Etsako, wani jami’in tsaro ya ware dan wakilin PREMIUM TIMES waje daya, ya shaida masa cewa maganar gaskiya Na’urar Tantance Katin Rajista ta lalace.

Daga nan sai ya ce masa an yanke shawara kawai jama’a su ci gaba da jefa kuri’a a haka.

Wannan ya bai wa ejan-ejan na APC da PDP dama rububin dattawa da gidadawa, su na nuna musu ‘yadda ake dangwala kuri’a.”

RIVERS
Wakilin PREMIUM TIMES ya ce a kan idon sa aka tayar da tunzuri a wata rumfar jefa kuri’a da ke karkashin Mazabar Bua Yhege cikin Karamar Hukumar Gokana. An rukume tsakanin magoya bayan APC da na PDP.
Yayin da na PDP ke cewa a kwashi kayan zabe zuwa kauyukan da ya kamata a rarraba su, su kuma magoya bayan APC na cewa ba su yarda a kai kayan zaben a cikin kauyukan yankin da suka ce ba, domin babu tsaro a kauyukan, kuma idan aka kai, to za a iya yin magudi.
An dai yi ta kiki-kaka, ga kayan zabe ajiye, amma rikici ya hana a dauka. Su kuma jami’an tsaro sun yi cirko-cirko, sun zuba idanu.

KARAMAR HUKUMAR BONNY

Akwai rumfuna da dama da ba a raba kayan zabe ba. Wani ya kwarmata wa wakilin PREMIUM TIMES cewa, wai wani dan siyasa ne ya je ya ce kada a raba kayan zaben.

ANAMBRA

Zanga-zanga ta barke a Mazabar Firamare da ke cikin Karamar Hukumar Awka ta Kudu. Jama’a ne suka harzuwa saboda na’urar tantance mai zabe ya na iya karanta katin rajista, amma kuma ko mutum ya dangwala, to ya dangwala banza, domin na’ura ba ta tantancewa.

ENUGU

Mazabar firamare ta Ezza Umuoma da ke cikin Karamar Hukumar Anininri an ci karo da matsala. Jami’in Zaben su ya shaida cewa sun samu matsakar kayan aiki, musamman tawwadar dangwale. Ya ce ba a hado musu da tawwadar dangwala kuri’a ba.

An kuma samu akasi, yayin da akwatinan zaben Dan Majalisar Tarayya aka lika musu takardar da ya kamata a lika wa akwatin zaben gwamna. Shi kuma akwatin Sanata aka lika masa takardar da ya kamata a lika wa akwatin dan majalisar jiha.

Sai dai kuma wakilin mu ya lura da wani jami’in zabe na ta gaganiyar warware wa masu jefa kuri’a wannan hardaddiyar mishkila.

OGUN

A Rumfar Zabe ta Ward 5, PU 006 kuwa da ke cikin Karamar Hukumar Ogbomosho, wakilin mu ya tabbatar da cewa har zuwa karfe 12: 56 ba a fara zabe ba. Su kuma jami’ai na jiran karfe 2 na rana ta yi, su rufe lokacin kada kuri’a.

WASU MATSALOLIN

Wakilan mu sun ruwaito matsaloli a wasu jihohi, kamar matsalar na’urar tantance masu zabe a jihar Anambra, a wata rumfar zabe da ya je. Sai matsalar rashin jami’in zabe na biyu, wato PO2 a wata rumfar zabe da sanatan Taraba ta Tsakiya yay i zabe a garin Ngoruje, da ke Karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba.

Share.

game da Author