Darektan hukumar NBMA Rufus Ebegba ya gargadi mutane cewa hukumar za ta rufe duk shagon da ta kama yana siyar da abincin da aka ingantashi da kimiyyar zamani a kasar nan.
Ya kuma ce hukumar ba za ta yi kasa kasa ba wajen ganin ta hukunta duk wadanda ke shigo da irin wadannan abinci kasar nan ba tare da izini ba.
Ebegba ya fadi haka ne da yake ganawa da PREMIUM TIMES ranar Talata inda ya kara da cewa daukar wannan mataki ya zama dole ganin cewa mutane sun yi ta kawo kuka cewa da gangar hukumar ta suke bari ake shigo da irin wadannan kayan abinci bayan sun san cewa ire-iren wadannan abinci na da matukar illa ga lafiyar mutane.
Ebegba ya ce daga yanzu duk shagon dake siyarwa ko kuma shigo da irin wadannan kayan abinci ba tare da izini ba zai fuskanci hukunci.
Idan ba a manta ba a shekarar 2015 ne Najeriya ta kafa dokar yin amfani da fasaha domin inganta abinci a kasan.
Hakan ya nuna cewa gwamnati ta amince a yi amfani da shi bayan an samu yardar haka daga humar ingancin abinci ta kasa cewa ba zai kawo wa mutane wani illa ba.