Za mu fara raba kayan zabe ranar 20 da 21 a jihar Kano – INEC

0

Hukumar zabe mai zaman kanta reshen jihar Kano (INEC) ta bayyana cewa za ta fara raba kayan zabe daga ranar Laraba 20 zuwa Alhamis 21 ga wannan watan a fadin jihar.

Jami’in hukumar zabe na jihar Riskuwa Arab-Shehu ya sanar da haka a yake zantawa da manema labarai a garin Kano ranar Talata.

Riskuwa ya bayyana cewa tun da INEC ta dage zaben suka tattara kayan da ke kasa zuwea Bankin Kasa dake Kano domin ajiya.

” Yanzu da INEC ta tsayar da ranar 23 ga watan Fabrairu ranar zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki na kasa zamu raba kayan aiki daga ranar Laraba zuwa Alhamis.

Riskuwa ya kuma kara da cewa hukumar zabe ta dauki wasu matakan da za su taimaka wajen gani aiyukkan zabe sun gudana yadda ya kamata.

Matakan sun hada ta samar da motocin da za a yi amfani da su wajen jigilar ma’aikata da kayan zabe, kammala horas da ma’aikatan wucin gadin da za su yi aiki ranar zaben.

PREMIUM TIMES ta bada labarin kalubalen da shugaban na INEC ya ce an fuskanta, wadanda tilas su ka sa aka dage zaben zuwa ranakun 23 Ga Fabrauru da kuma 2 Ga Maris.

Kungiyoyin rajin kare dimokradiyya irin su CDD, sun nuna tsananin damuwa ganin cewa yawancin kayan zaben duk an rigaya an tura su jihohi da kananan hukumomi kafin a soke zaben.

A kan haka ne INEC ta dawo da kayan zaben da aka rigaya a ka raba. Cikin jihohin da aka maida na su din akwai Lagos, Anambra, Enugu,Barno,Kano,Gombe da Filato.

Share.

game da Author