Yunwa ta haddasa wa masu gudun hijirar daga Baga yin zanga-zanga a Maiduguri

0

Daruruwan ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya tarwatsa daga Baga sun tsere zuwa cikin garin Maiduguri, inda suka mamaye babban titi su na zanga-zangar rashin cin abincin na tsawon kwanaki da ba su yi ba.

Sun hau kan titin da ya tashi daga Maiduguri zuwa Damaturu, sun a zanga-zangar yadda gwamnati ta yi watsi da su.

Sai da ta kai an rika jefa musu barkonon tsuhuwa ganin cewa sun fara kakkarya kaya, musamman ma allunan da ke dauke da fastocin ‘yan takarar siyasa.

Sun kuma yi dandazo a daidai shataletalen Bulunkutu, inda hakan ya haifar da cinkoson motoci cikin garin, saboda masu zanga-zanga sun tare hanyoyi.

An ga yadda sojoji da ‘yan sanda suka isa wurin domin shawo kan matsalar cinkoson motoci, amma masu zanga-zangar suke ce ba za su matsa ba har sai gwamnati ta biya musu bukatar su ta abinci da sauran abubuwan bukatun rayuwar su na yau da kullum tukunna.

Masu gudun hijirar sun tsere ne daga garin Baga wanda Boko Haram suka kai wa hari cikin watan Janairu.

Duk da a baya sojoji sun ce an kori Boko Haram daga garin, wasu masu gudun hijira sun shaida cewa har yanzu Boko Haram na cikin garin.

Share.

game da Author