Yan takife sun babbake gidan Abba, dan takarar gwamnan Kano na PDP

0

Wata sanarwa da kakakin yada labarai na dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PDP ta fitar, ta ce an banka wa daya daga cikin gidajen sa wuta a Kano.

Sanarwar wadda Dawakin Tofa ya sa wa hannu, ta ce dan takarar, Abba Yusuf ya yi zargin cewa magoya bayan jam’iyyar APC ne su ka cinna wa gidan wuta, wanda ke cikin unguwar Chiranci, a Karamar Hukumar Gwale, cikin birnin Kano.

Sun kuma kara da cewa daya daga cikin hadiman shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, mai suna Junaidu Abdulhamid ne ya jagoranci tawagar matasa 60, suka je su ka banka wa gidan wuta.

PDP ta ce akwai wani rikakken dan APC mai suna Habibu Dandayis, wanda suka ce da shi aka je wurin banka wa gidan wuta.

An bada rahoton cewa an yi kaca-kaca da gidan wanda dama an maida shi ofishin siyasa, kuma aka kone mota guda daya kirar Golf – III da ke kofar gidan.

Wani da aka kai harin a kan idon sa, ya ce ‘yan takifen da suka kai harin, su ne dai suka kai wa magoya bayan Kwankwasiyya hari a Hawan Daushe, lokacin shagulgulan Babbar Sallah a Kano.

Share.

game da Author