A ranar Litini ne kakakin ‘yan sandan jihar Akwa Ibom Macdon Odiko ya bayyana cewa rundunar ta kama wasu mutane 10 da ke da hannu a bankawa motocin INEC 11 wuta a kauyen Obot dake karamar hukumar Akara.
Odiko ya ce INEC ta samar da wadannan motoci ne domin jigilan kayan zabe zuwa bangarorin jihar.
Ya kuma ce wadannan mutane sun banka wa wadannan motoci wuta ne a ofishin INEC ranar 15 ga watan Fabrairu da karfe 10:05 na dare sannan sun kashe wani mutum da har yanzu ba a san ko wanenene.
” Mun kama su dauke da bindiga daya, harsashai, layuka, kwalin ashana biyu, giya, almakashi daya, adda biyu da kullin wiwi’’.
Odiko yace rundunar ta aika da su Inda ake hukunta masu aikata laifuka irin haka domin ci gaba da yin bincike akai.
Bayan haka rundunar ta kara kama wasu mutane 41 ranar jajibirin zabe a Otel din Angeline dake kusa da makarantar ‘Dove International School’ dake Uyo.
Odiko ya ce wadannan mutane sun bayyana cewa sun zo jihar ne daga jihohin Bayelsa, Delta da Ondo domin sa ido a zaben da za a yi a jihar amma sai Basu iya nuna wani abu da zai nuna su masu sa-ido a Zabe bane.