‘Yan sanda sun kama wani mutum dauke da takardun ‘zabe na boge’ a jihar Sokoto

0

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto Muhammad Sadiq ya bayyanq jami’an ‘yan sanda sun kama wani mutum mai suna Shehu Maidamma dauke da takardun zabe na boge’.

Sadiq ya fadi haka ne da yake zantawa da manema labarai a garin Sokoto ranar Litini inda ya kara da cewa sun kama Shehu dauke da wadannan takardu ne ranar Lahadi.

Ya ce hukumar zabe mai zaman kanta na jihar (INEC) ta tabbatar musu da cewa wadannan takardun da Shehu ke dauke da su takardun boge ne. Sannan bincike ya kara tabbatar wa rundunar cewa takardun jam’iyyar PDP ce ta buga su Kula domin nuna wa masu Zabe yadda zasu zabi Jam’iyyar.

” Ina kira ga mutane da su kwantar da hankalinsu domin jami’an tsaro na aiki da hukumar INEC sau da kafa domin ganin cewa zabe ya gudana cikin kwanciyan hankali.

Jami’in INEC Muhammad Musa ya tabbatar da haka inda ya kara da cewa wadannan takardun zabe da aka kama Shehu da su ba ainihin takardun zabe bane.

Ya ce tabas jam’iyyu na da damar wayar wa magoya bayan su kai game da yadda za su kada kuri’a amma bisa ga doka kamata ya yi a tsayar da duk wasu aiyukkan kamfen da karfe 12 na daren Juma’a.

Har yanzu dai jam’iyyar PDP batace komai ba akai.

A ranar Asabar ne aka dage zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa zuwa ranar 23 Ga Fabrairu.

Share.

game da Author