Rahotanni sun tabbatar da kashe ‘yan Boko Haram biyar da sojojin Najeriya uku a wani gumurzu da suka yi a Buni Yadi da ke cikin Karamar Gujba a cikin Jihar Yobe.
An yi wannan fadan ne a ranar Asabar da ta gabata.
Sabon Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Sagir Musa ne ya tabbatar da haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Kanar Musa ya ce gumurzun ya faru ne a daidai lokacin da Boko Haram Haram suka kai wani samame a sansanin sojoji da ke Buni Yadi.
Makarantar Horas da Zaratan Sojoji da ita da Bataliyar Sojojin Burget na 27, duk a Bunu Yadi su ke.
Musa ya ce akwai kuma wasu sojoji biyar da suka jikkata da a yanzu haka ake kan kula da lafiyar su.
Ya ce Boko Haram da su ka kai harin, sun kai farmakin ne a cikin motoci masu budadden baya har guda hudu, masu daukar manyan bindigogi samfurin mashin-ga, wato tashi-gari-barde.
Ya ce kuma sun je da mota mai sulken hana lahanin tashin nakiya da manyan bindigogin da ake yi wa zabarin jigidar harsasai.
Sannan ya bada sanarwar cewa an kwaci wasu makamai masu dama daga hannun su.
Ya kuma ruwaito cewa Hafsan Hafsoshin Najeriya Janar Tukur Buratai ya jinjina wa sojojin da suka fatattaki Boko Haram din, da ma sauran wadanda suka yi gumurzu da su a baya bayan nan.
A karshe ya kuma gode wa wadanda suka yi gaggawar shaida wa sojoji rahoton cewa akwai alamomin Boko Haram za su hari.
Discussion about this post