Shugaban gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jinya na Najeriya (JOHESU) Josiah Biobelemoye ya bayyana cewa kungiyar ta ba gwamnati wa’adin kwanaki bakwai domin ta biya bukatun ta ko ta fara yajin aikin duk Kasa.
Biobelemoye ya fadi haka ne a taron tattauna matsalolin da kungiyar ke fama da su a fannin kiwon lafiyar kasar nan da ta yi da kungiyar kwadago a Abuja.
“Bukatun mu da gwamnati ta kasa biya sun hada da rashin biyan ma’aikata albashin watannin Afrilu da Mayun 2018, rashin biyan ma’aikata albashi da sabon tsari na CONHESS, rashin amincewa ma’aikatan jinya shugabantan wasu bangarorin aiki a asibitoci da dai saran su.
Biobelemoye ya ce kungiyar ta yarda ta bada wa’adin kwanaki bakwai ne saboda rokon kin shiga yajin aiki da malaman addinai suka rika yi mata sannan da tausayin halin da marasa lafiya za su shiga idan kungiyar ta fara yajin aikin.
Ya ce da zaran wa’adin da kungiyar ta ba gwamnati ya cika za ta mika ta ga kungiyar NLC.
A karshe shugaban kungiyar NLC Ayuba Wabba ya ce kungiyar ya tsara wasu hanyoyi da za su taimaka wajen tursasa gwamnati wajen yin abin da ya kamata.
Ya ce yin haka ya zama dole ganin cewa gwamnati bata bi hukuncin da kotu ta yanke ba ta yi gaban kanta wajen yin amfani da dokar ba aiki ba albashi ga ma’aikatan jinya sannan ta biya likitoci albashinsu su.