Yadda sabon hargitsi ya ci rayuka da dama a Kajuru – Inji wadanda suka tsira

0

Wani sabon hargitsi ya barke a Karamar Hukumar Kajuru, Jihar Kaduna, wanda har zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadin wadanda aka kashe ba.
Wata ’yan asalin yankin mai suna Paulina Irimiya, ta ce an kai harin ne da misalin karfe 6:30 na safe.

Paulina wadda ke magana cikin firgici da kidimewa, ta yi zargin cewa Fulani ne suka kai musu harin.

Yankin Kajuru ya zama abin maida hankula kan sa tun bayan rikice-rikicen da suka rika faruwa a kai a kai, da ke haifar da mummunan kashe-kashe.

Gwamna Nasiru El-Rufai ya bayyana kazamin harin da aka kai a rugagen Fulani cikin makonni biyu da suka gabata, cewa an kashe Fulani 130.
Harin da aka kashe Fulanin masu tarin yawa dai kabilun yankin ne su ka kai shi.

A yau Talata da safe kuma, Gwamna El-Rufai na Kaduna ya tabbatar da wannan sabon harin da aka kai.

Ya sanar da haka ne ta bakin kakakin yada labaran sa, Samuel Aruwan.

Sanarwar ta ce wannan sabon harin ya fantsama har cikin Karamar Hukumar Kachia, wadda ke makautaka da Kajuru.

Gwamnan ya tabbatar wa jama’a cewa jami’ann tsaro nab akin kokarin su wajen ganin sunn shawo kan rikicin.

“Gwamnati da damu kwarai da wannan sabon hari, ta yi Allah-wadai da shi, kuma ta na kira ga jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro wajen kare lafiyar al’ummar yankin.”

DAGA GANAU BA JIYAU BA

Paulina Irimiya da ke zaune a kauyen Maro Karami, cikin Karamar Hukumar Kajuru, ta ce an fara kai harin ne tun da karfe 6:30 na safiyar yau.

Ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ita da wasu makwautan ta na cikin coci, sai kawai suka rika jin karar harbe-harben bindigogi.

Ta ce jin haka sai kawai kowa ya fice daga cocin a guje.

Ta ce maharan wadanda aka tabbatar da cewa Fulani ne, sun banka wa gaba dayan kauyen na su wuta.

Ta kuma kara da cewa Fulanin sun rika bin wadanda suka tsere a cikin daji su na harbi da bindigogi.

Paulina ta ce ba za ta iya cewa ga mutane nawa aka kashe ba. Sai dai kuma ta ce gaba dayan ‘yan uwan ta ba ta san halin da suke ciki ba.

“Ni dai na gudu ina kan hanyar tafiya neman mafaka a wani kauye. Amma dai kashe-kashen ya lafa yayin da sojoji suka isa wurin.

Wata da ke zaune a kauyen, mai suna Racheal, ta ce da idon ta dai ta ga gawarwaki shida.

Ta ce Fulanin sun yi wa kauyen dirar-mikiya da sassafe, su ka ce su na neman shanun su ne, amma bayan dan lokaci sai cigiya ta koma harin-bazata.

“An kone gidaje masu yawa, ciki har da cocin da mata ke bauta a lokacin da suka kai harin.

“Ni a yanzu haka da na ke magana da ku, an kashe kawu na da kaka na. Na kuma ga wasu gawarwaki hudu da ido na.” Inji Racheal.

Sai dai shi kuma Shugaban Kungiyar Kudancin Kaduna mai suna Solomon Musa, ya ce wannan sabon rikicin ya ci kauye guda da abin da kwe cikin sa.

“Majiya mai yawa ta shaida mana cewa an yi raga-raga da kauyen gaba dayan sa.

Ya ce ba zai iya tantance yawan wadanda aka kashe ba, saboda cikakkun bayanan da ya kamata ya samu daga dagatan yankin, ba za su samu ba a yanzu. Ya ce dagatan yankin su na hannun jamai’an tsaro, an kame su.

Shi kan sa kakakin yada labarai na ‘yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa bai ji labarin barkewar sabon rikicin ba.

Sai dai kuma ya ce da zarar ya tantance, zai tuntubi PREMIUM TIMES da karin bayani.

Wasu na ganin wannan hari ne na ramuwar gayya Fulani suka yi, kasancewa an kashe musu ‘yan uwa har 130 a cikin wasu rugage takwas.

An dai dora laifin kisan Fulanin a kan kabilar Adara, mazauna yankin, wadanda shi kan sa Kwamandan Bataliya ta 1 da ke Kaduna ya tabbatar da cewa an rika kwantar da Fulani 37 a gefen wani rafi aka yi musu yankan-rago.

Share.

game da Author