Ranar Litinin aka tozarta Shugaba Muhammadu Buhari a filin wasa na Mashood Abiola da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Hakan ta faru ne a lokacin da jam’iyyar APC ke kamfen din neman zaben ta. Ba Buhari kadai aka tozarta a wurin taron ba, har da Shugaban APC, Adams Oshiomhole wanda shi ma ya sha jifa da duwatsu da ledojin ‘pure water.’
Rincimi ya barke ne bayan da Gwamna Amosun ya gama jawabi, ya damka makirho a hannun Adams Oshiomhole.
Cikin jawabin na sa, Amosun wanda gwamnan APC ne, ya yi kiran da a zabi Buhari a zaben Shugaban Kasa, amma idan an zo zaben gwamna, to a zabi Adekunle Akinlade na APM, kada a zabi Dapo Abiodun na APC.
Ya ce idan Akinlade ya ci zabe, to zai iya komawa APC daga baya.
Ko da Oshiomhole ya karbi makirho ya fara jawabi, sai kawai aka rika cewa “barawo, barawo”. Kafin a ankara, sai hasallallu suka fara jifan Oshiomhole da duwatsu da ledojin ‘pure water’.
Kafin sannan kuwa tuni magoya bayan APC da na APM sun yi fito-na-fito dauke da muggan makamai, har suka yi wa junan su jina-jina.
Bayan Oshiomhole ya sha jifa yayin da ya nemi daga hannun Dapo Abiodun a matsayin dan takarar PDP.
Wuri ya yamutse bayan duk wani hakuri da Gwamna Amosun ya yi domin a daina yamutsi ya ci tura.
Wasu tsoffin gwamnoni da masu ci a yanzu da suka tsere daga kan mimbarin kamfen, sun hada da Bola Tinubu, Segun Osoba, Bisi Akande, Rotimi Akeredolu da Kayode Fayemi da Ambode na Legas.
Hasalallu sun rika jifar Buhari a lokacin da ya daga hannun Dapo Abiodun sama.
Sai da jami’an SSS suka yi wa Buhari kawanya don kada a ji masa rauni.