Wasu likitoci daga jami’ar Havard T.H Chan dake Boston kasar Amurka sun gano cewa cin aya,gyada,gasashshen ya’yan kashu, Almond na taimakawa wajen hana mai dauke da cutar siga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya.
Shugaban wadannan likitocin Gang Liu ya bayyana cewa sun gano haka ne a binciken mahimmancin da wadannan ‘yayan itatuwa ke yi a jikin masu fama da wannan cuta.
Liu ya ce binciken da suka yi ya nuna cewa aya, gyada, gasashshe ‘ya’yan kashu da Almond na dauke da sinadarin dake kara karfin zuciyar mutum.
Binciken ya kuma nuna cewa idan mai dauke da cutar siga (Diabeties) na cin irin wadannan ‘ya’yan itatuwa ya na samun kariya matuka.
Liu ya yi kira ga masu dauke da cutar siga da su rika cin wadannan abubuwa domin samun lafiya da kariya daga kamuwa da wannan cuta.
Cutar siga na kama mutum ne idan aka samu matsala da wasu daga cikin ababen da ke sarrafa abincin da muke ci a cikin mu.
” Shi Insulin ya na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki. ”
A dalilin rashin aikin ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da cutar siga.
Likitocin sun bayyana cewa ciwon siga na kawo makanta, hana karfin mazakuta a namiji,kawo cutar hawan jini da cututtukan dake kama zuciya.
Likitocin sun kuma ce yawan shan abubuwa masu zaki, yawan cin abincin dake dauke da sinadarin ‘carbonhydrates’, kiba a jiki, rashin motsa jiki, shan giya na sa akamu da wannan cuta.
Discussion about this post