Tirka-tirka da ta faru a ranar Lahadi da dare, ta yi munin da washegari Litinin ta zama dambarwa a Jihar Imo.
Abin da ya faru shi ne, yadda aka takure babban jami’in zabe na Mazabar Sanatan Imo ta Yamma, aka tsare shi har wasu ‘yan kwanaki.
Shi ne ya bayyana haka da kan sa, a lokacin da ya ke bayyana sakamakon zaben shiyyar sanatan, wadda Gwamna Rochas Okorocha ya fito takara.
Kafin ya kai ga bayyana sakamakon zaben a ofishin INEC na garin Orlu, Farfesa Ibeabuchi, ya ce an tirsasa shi tilas ya bayyana sakamakon.
“Jama’a, suna na Ibeabuchi Izuchukwu Innocent, kuma ni farfesa ne Jami’ar Fasaha ta Owerri. Ni ne kuma Babban Jami’i mai lura da zaben Sanatan Shiyyar Imo ta Yamma.” Inji shi.
TONON SILILI
“Ina sanar da ku cewa tsare ni aka yi tsawon kwanaki. To zancen gaskiya ina da tsananin bukatar zuwa gida domin na ga iyali na da ‘ya’ya na. Dalili kenan zan bayyana wannan sakamako a bisa tilas, ba da son raina ba.”
Daga nan sai fara karanto sakamakon zabe.
KWATAGWANGWAMA
Bayan da ya bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi 9 daga cikin wadanda su ne su ka kunshi shiyyar sanata din. Sai Ibeabuchi yay i cak, ya daina magana, yay i shiru.
A lokacin da yay i shiru din, karfe 9:45 daidai.
A lokacin kenan ana jiran sakamakon zabe daga kananan hukumomi uku, wato Orlu ta Yamma, Ugwuta da kuma Orlu.
Gwamna mai barin gado, Rochas Okorocha, shi ne ya lashe kananan hukumomi 8 daga cikin 9 da aka bayyana.
Kawai sai aka ji Ibeabuchi ya ce an yi masa wani kira na gaggawa cewa ya hanzarta ya koma Owerri, amma washegari da safe zai dawo ya ci gaba da bayyana sakamakon zabe.
Ya ce Kwamishinan Zabe ne na Jihar Imo, Francis Ezeonu ya yi kiran sa.
Ai kuwa nan take sai magoya bayan Okorocha suka ce bai fa isa ya bar wurin ba, har sai ya kammala bayyana sakamakon sauran kananan hukumomin uku tukunna.
Nan take su ka tare, suka yi cacukui, su ka hana farfesan ficewa, duk kuwa irin kokarin da ‘yan sanda suka yi domin shiga tsakani.
Aka shafe sa’o’i da yawa, tun magoya bayan Okorocha, wato ejan na jam’iyyar sa ta APC su na surfa wa farfesan ashariya, har suka dawo su na magiya da lallashi, amma farfasan nan ya ce ba zai bayyana ba.
Duk da Okorocha da abokin karawar sa sun je wurin bayyana sakamakon zaben washegari Litinin da safe, a lokuta daban-daban, hakan bai sa Farfesa Ibeabuchi ya sauko ya hakura ya bayyana sakamakon ba.
A karshe dai bayan an kwana, Ibeabuchi ya hakura ya bayyana sakamako cewa Okorocha ya yi nasara da kuri’u 97,762, shi kuma Onyeriri ya samu 63,117.
ME YA YI ZAFI NE?
Ba a dai san dalilin da ya sa Ibeabuchi ya ki bayyana sauran sakamakon a ranar Lahadi da dare ba, amma kuma washegari da aka matsa masa lamba ya bayyana.
Yayin da PREMIUM TIMES ta tambayi kakakin INEC na jihar, Emmanuella Opara ta ce INEC na bibiyar lamarin, kuma an tura jami’an tsaro su je su zo da farfesan zuwa Owerri.
Onyeriri ya shaida cewa magoya bayan Okorocha ne suka rike shi domin tilasta shi ya bayyana sakamakon zaben da Kwamishinan Zabe ya ce masa kada ya bayyana.
Ya ce Ibeabuchi ya tsaya ya daina bayyana sakamakon zaben ne bayan da ya lura da cewa an tabka aringizo inda aka kara wa Gwamna Okorocha dubban kuri’u.
Onyiriri wanda dan majalisar tarayya ne, ya ce ba zai taba amincewa da sakamakon zaben ba.
Dama kuma wakilin PREMIUM TIMES ya ruwaito labarin da ya bayyana yadda aka ci zarafin wakilan jaridun da suka je daukar labarin zaben, kuma aka tsare su tun da sassafe har zuwa karfe 10: 14 na safe.