A jiya Lahadi ne Gwamnan Jihar Jigawa Mohammed Badaru ya kwashi buhun kunya a hannun mazauna Karamar Hukumar Gagarawa, yayin da aka kaurace wa halartar wurin kamfen din na sa.
An shirya zangamin ne domin gwamna ya je Gagarawa neman ci gaba da mulkin jihar a karkashin jam’iyyar APC.
Badaru, wanda ya kaddamar da fara kamfen din sa a Guri da Hadejia a ranar 21 Ga Janairu, bai sha da dadi ba a garin Gagarawa a jiya Talata.
PREMIUM TIMES ta binciko cewa mutanen Gagarawa su na cike da haushin Badaru, saboda ya kwace musu gonaki ya damka ga wani kamfanin noman rani na kasar Chana.
Idris Garin-Ciroma, wani mazaunin yankin, ya shaida wa wakilin mu cewa gwamnatin jihar Jigawa ba ta ba su kudaden diyyar da suka taka kara suka karya ba.
“Dalili kenan muka ce ba za mu je wurin kamfen din sa ba. Ya bai wa baki gonakin mu kuma bai biya mu kudin kirki a matsayin diyya ba.”
Badaru ya yi kokarin ya ga ya kare kan sa a lokacin da ya ke jawabi ga kalilan jama’ar da ta je ta saurare shi.
Ya shaida musu cewa ya sani su na fushi ne saboda gonakin su. Daga nan sai ya ce idan suka yi hakuri, abin zai zame musu alhari nan gaba kadan, kuma za su yi farin ciki.
Ya buga misali da yadda mutanen yankin Kura suka rika jin haushin tsohon gwamnan Kano Audu Bako, saboda ya shigo da tsarin noman rani a Kadawa.
Badaru ya ce yan zu ga shi nan a Kura ta na daya daga cikin yankin da aka fi noma shinkafa a kasar nan.
Sai dai kuma yayin da gwamnan ke jawabi, sai wasu matasa suka yi cincirindo a Garin Ciroma, da niyyar su yi wa Badaru kofar-raggo.
Amma ba su yin nasara ba, domin an gaggauta sanar da tawagar gwamnan, inda hakan ta sa suka canja hanyar ficewa daga garin.
Hakan ta faru a Kazaure kwanan baya, inda aka yi wa tawagar gwamna ruwan duwatsu a kauyen Dandi, har sai da ta kai Dan Majalisar Tarayya Nuhu Gudaji ne ya yi sauri ya shige gaban tawagar gwamna, ya rika bai wa jama’a hakuri.
A fadar Sarkin Kazaure, Mai Martaba Sarki Najib Hussein ya yi wa gwamna kofarin cewa al’ummar yankin su na fushi da jami’an gwamnatin sa.
Ya kuma roke shi a gagauta shawo kan lamarin tare da gayra titin da ya tashi daga Kazaure zuwa Roni, wanda Sarki Najib ya ce ya dade a lalace.
A Gwaram ma an yi wa tawagar Badaru eho da muzantawa a lokacin da sanatan yankin, Sabo Nakudu ya hau mimbari ya na magana.
Mutanen yankin sun yi korafi da shi snatan sosai, kuma kujearar sa ce matashin dan takara, kuma dan Sule Lamido, mai suna Mustapha Lamido ke nema shi ma.