Hukumar Shige da Fice ta kasa (NIS) ta ceto ‘yar wata tara da wasu yara kanana 10 da ake kokarin safarar su zuwa kasar Libiya a jihar Katsina.
Jami’in hukumar Ajisafe Olusola ya sanar da haka wa manema labarai a garin katsina ranar Laraba.
Olusola yace hukumar ta kama Deborah Adewunmi mai shekaru 29 da Moriliya Ibrahim mai shekaru 31 a dalilin alakar da suke da shi wajen kokarin fdicewa da wadannan yara ranar 11 ga watan Faburairu.
Ya ce sun yi nasarar kama wadannan mutane ne bayan bayanan sanar musu da aka yi a boye kafin su aikata hakan.
Olusola yace bincike ya nuna cewa wadannan mata na tafe ne da wadannan yara zuwa kasar Libiya ba tare da takardun tafiya ba na gaske ba.
” Asirin su ya tonu ne bayan ganowa da muka yi cewa daga jihar Katsina za su yada zango ne a garin Agadez na kasar Nijar inda za su hadu da mijin daya daga cikin matan domin su karisa zuwa kasar Libiya.
” Dubun su ya cika ne a lokacin da kudin guzirin su ya kare inda basa iya ciyar da kansu da wadannan yara.”
A karshe Olusola yace hukumar za ta danka wadannan mata ga hukumar dake bibiyan masu aikata iurin wannan laifi domin hukunta su.