Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshimhole, ya yi kiran da a yi wa jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC garambawul.
Ya yi wannan kiran ne a yau a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, wanda suka gudanar a yau Litinin a Abuja, wanda cikin mahalarta har da Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne dan takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.
Shi ma Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya halarci taron.
Oshiomhole ya yi zargin cewa akwai wasu Kwamishinonin Zabe da ke wa jam’iyyar PDP aiki.
Ya fito gaba-gadi ya ambaci sunan Kwamishinan Zabe na Jihar Akwa Ibom, Mike Igini.
Idan ba a manta ba, shi kuma Mike Igini ya tara manema labarai ya yi musu korafin cewa wasu batagarin ‘yan siyasa na neman dagula harkar zabe.
Ya yi wannan kakkausan kalamin ne bayan da hargitsin da ya tashi a lokacin da aka tattara motocin daukar kayan zabe a jihar Akwa Ibom, aka yi yamutsin da har aka kona motoci 13.
Igini dai bai ambaci ko wace jam’iyya ce batagarin ‘yan siyasar su ke ba.
PREMIUM TIMES ta kawo muku labarin banka wa motocin 13 wuta a Jihar Akwa Ibon tun a labaran da ku ka karanta a ranar Asabar.
“Abin takaici ne a ce ‘yan siyasa wadanda su ne ke fin kowa cin moriyar dimokradiyya, ya kasance kuma su ne a sahun gaba wajen neman kawo mata barazana.” Haka Igini ya furta a ranar Asabar.
Ya ce babu wani dan siyasa da zai iya bude masa kunne ko ya cika masa ido domin ya kauce daga yin abin da dokar INEC ta gindaya masa.
Igini dai fitaccen dan taratsin kungiyoyin rajin kare jama’a ne, kuma shi ne Kwamishinan Zabe Mai Lura da Jihar Akwa Ibom.
Shi kuma Oshimhole, a yau ya kwatanta wasu jami’an INEC tamkar sawu alkalan wasa, wadanda idan wata kungiyar kwallon kafa ta yi korafin nuna bambanci a alkalancin su, to sai a canza alkalin wasan.
Sannan kuma ya zargi INEC da laifin kwarmata wa jam’iyyar PDP yiwuwar dage zaben shugaban kasa.
Da yake magana bayan Oshimhole ya kammala na sa jawabin, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tilas INEC ta yi aiki ingantacce a cikin nuna dattako. Kuma kada ta bari mutuncin ta ya zube.
“Akwai dokokin kasa da suka bai wa INEC kariya. Amma fa kada su rika wasa da hankalinmu.” Inji Buhari.