Wa ne ne Salahaddeen a tarihin Musulun ci? – Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Wa ne ne Salahaddeen a tarihin Musulun ci? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Wa ne ne Salahaddeen al-Ayyubi (532 – 589 AH)? Salahudden shi ne ake yiwa kirari a musulunci da Sarki Mai Nasara , Abul –Muzfar Salahuddin Yusuf Ibn Ayyub Ibn Shazi Ibn Marwan Ibn Yakub, al-Duwaini al- Tikriti. Ya shahara da sunan Salahaddeen wal –Dunya ( mai gyara Addini da duniya), Sarki na farko a Kasar Masar da Sham (Egypt da Syria). Ya assasa daular Ayyubiyya. Mabiyin Mazhabar Shafi’iyya, mai tsantsene da zuhudu kuma Cikkaken Ahlus- Sunnah, Sufi kuma dan kabilar Kurdish, babban kwamandan sojojin Musulunci a zamaninsa karkashi daular Abbasiyya. An haifi gwarzon soja Salahuddin Al-Ayyubi a Miladiyya ta 1138, a yankin Tikrit da ke Kasar Iraqi a yau. Kuma ya yi wafati a Damascus da ke Syria Miladiyya ta 1193.

Mahaifin Salahaddeen Al-Ayyubi gwamna ne a jahar Tikrit, kuma salihin bawan Allah ne. Salahuddin Al-Ayyubi ya ta so ne a Damashk inda ya hardace Al-Kur’ani, ya yi karatun Fiqihu da Hadisi da Adabi mai zurfi. Ya yi yaki a matsayinsa na Mujahidi har yakai matsayin babban kwamanda. Jan garzo ne, ma sanin addini, mai gudun duniya, kwararre a yaki. Yana da sa’a a filin daga ga kuma hikimar gudanar da mulki cikin adalci da dai-daito. Mai tsoron Allah ne da gudun duniya. Yayi muki kimanin shakaro 20. A zamaninsa harkokin cikin gida sun dai-daita kuma ya yi burki ga gamayyar mayakan Kafirai da suka kashe musulmi sama da mutum dubu sittin.

Sarki Salahuddin Al-Ayyubi ya sadaukar da rayuwarsa a kan jihadi domin yadawa da kare kima da martabar musulunci har mutuwarsa. Be tara
abin duniya ba. An ruwaito cewa ya rasu yabar Dinare Daya da Dirhami Arba’in da bakwai. Ya kasance Sufi ne mai Takawa har ya kwanta dama.

GUDUN MUWAR SADAUKI SALAHUDDIN AL-AYYUBI GA MUSULUNCI

Jarumta, ilimi, da basirar siyasar Salahuddin Al-Ayyubi sun yi tambari a duniyar musulunci kuma ya samu nasarori azamaninsa kamar
haka:

1) Gina makarantu masu yawa, har yakasance Musulmai basu bukatar doguwar tafiya domin neman ilimi. A kowane gari akwai makaranta da malamai kuma ga albashi mai tsoka ga kowane malami.

2) Inganttacen alkalanci, ya nada nagartattun alkalai, domin wanzar da adalci. Kuma ansamar da kotuna na musamman domin gunanar da hukunci a cikin matsalolin sojoji da Jihadi.

3) Fadar Salahaddeen cike take da manyan malamai masu bada fatawa kuma ya na tattauna matsaloli da su domin gudanar da mulkin adalci a
zamaninsa. Malamai su ne mashawarta kuma kwamandojin soji, sannan kuma su ne a matakan mulkin gwamnati daban-daban.

4) Hada kan al-umma, Salahaddeen ya sami al-umma a watse cikin rauni da rashin hadin kai. Da taimakon Allah ya hada kan al-umma ta donkule a
guri daya.

5) Bunkasa fagen ilimi, bude makarantu da martaba malaman da Salahuddin ya yi da kula da matsayinsu tare da damawa dasu a cikin
mulki ya bada nasar bunkasa ilimi da habbaka shi ta kowane bangare.

6) ‘Yanta Masallacin Kudus daga kafirai, ya jagoranci yakar azzaluman Yahudawa da Kiristoci a zamaninsa kuma ya kwato Masallaci Kudus da
wasu yankunan palasdinu daga hannun kafiran duniya.

7) ‘Yanta musulmin duniya daga gamayyan Kiristoci, kafin darewar Salahuddini karagar mulki Kristocin duniya sun hada sojojin gamayya
masu dumbin yawa, suna ta yakin musulmai. An ruwaito cewa sun kashi musulmi sama da 60,000 a cikin yakin (wato Crusade). Salahuddin shi ne mujahidin da ya ci nasara wajen tarwatsa makiyan.

8) Tsaftace Kudus daga dukkan shirka, bayan kwato Kudus daga hannun Kafirai, an tsafatce sa daga dukkan alamonin shirka kuma aka yi
gyare-gyare daga gine –gine domin kiwon lafiya da inganta rayuwar musulmi a cikinsa.

Ya Allah ! ka yarda da wannan bawa naka, kasa shi a aljannar ka. Amin

Share.

game da Author