Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya sha kayi a mazabar sa inda ya tashi da kuri’u 5i kacal cikin daruruwan mutanen da suka kada kuri’a wannan mazaba.
Uba Sani na jam’iyyar APC ne ya lashe mazabar da kuri’u sama da dari biyu. Shi kuma Lawal Adamu na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 34.
A wata mazabar kuma Uba Sani ya lashe zaben da kuri’u 292. Ana ci gaba da tattara sakamakon zabe a mazabu dabam-dabam a fadin kasar nan.

Discussion about this post