Tsoffin Janar-Janar 71 sun goyi bayan Buhari ya zarce

0

A ranar Litinin ne tawagar tsoffin Janar-Janar na sojoji su 71 suka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyarar nuna goyon baya.

Tawagar wadda ke karkashin jagorancin Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, sun je ne kuma suka jaddada wa Buhari cewa za su yi iyakar kokarin su wajen mara masa baya ya yi nasara a ranar 16 Ga Fabrairu.

Buba Marwa ya yi gwamnan mulkin soja a jihohin Barno da Lagos. Ya ce su na wakilcin tsoffin Janar-Janar har kashi 99.9 bisa 100 na kasar nan.

Sun kara da cewa abin alfaharin su ne tsohon soja dan uwan su ya na kyakkyawan shugabancin da ake yabawa.

Sun kuma yi bayanin cewa Buhari ya yi rawar gani wajen alkawurra uku da ya dauka na kashe cin hanci da rashawa, tsaro da kuma tattalin arziki.

Da ya ke jawabi, Buhari ya gode musu kwarai, kuma ya ce zai kara himma. Ya sake tuna masa abin da ya fada a lokacin da ya na shugaba na mulkin soja cewa “ba mu da wata kasa sai Najeriya.”

“Sai mu kara yin godiya ganin yadda a baya an yi Yakin Basasa, tsawon watanni 30, wanda ya ci rayuka milyan 2. Amma duk da haka har yau kasar nan ta na dunkule wuri daya.

Share.

game da Author