Kotun Daukaka Kara dake jihar Sokoto ta amince wa jam’iyyar APC da duka ‘yan takarar ta su fafata a zabuka masu zuwa. a jihar
Bayan haka ta Umarci hukumar zabe da ta amince da duka ‘yan takaran da jam’iyyar ta mika mata.
Wannan hukunci da Kotun ta yanke ya ba jam’iyyar daman fafatawa a zabukan Majalisun Kasa da na jiha sannan kuma da na gwamnan jihar.
Alkalai uku da suka saurari karar sun ce sun yi watsi da daukaka karar da aka yi ne bayan wanda ya shigar da daukaka karar Aminu Jaji ya janye karar.
Yanzu ya rage ga hukumar Zabe ta bayyana matsayin ta game da wannan hukunci wanda dai akwai tabbacin cewa APC a jihar Zamfara ta sha.
Discussion about this post