Sumayya ta tattauna da PREMIUM TIMES kan yadda masu garkuwa suka yi garkuwa da ita da wasu kawayenta wato ‘yan biyun nan da aka sace a jihar Zamfara.
Abin takaici, tausayi da tsoro, dalla-dalla Sumayya ta bayyana mana yadda ta shafe sama da wata daya a hannu masu garkuwa da mutane a dajin Zamfara
PT: Yaya wadannan masu garkuwa da mutane suka kama ki?
Sumayya: Masu garkuwa sun zo gidan mu a daren Talata da karfe 11:30. A lokacin da ni da ‘yan biyu. Bayan mun yi shinfidan mu mun kwata a tsakar gida. Daga nan ne sai na ji ana kwankwasa kofar gida. Da na ji haka sai dauka mazan makwabta ne suka zo hira wajen ‘yan biyu dake tare da ni.
Zuwa can da na ji kwankwasa kofa ta yi tsanani babu kakkautawa sai na tada ‘yan biyun, na ce musu kai kuat shi mu shiga cikin dakin mijina domin wannan buga kofa ba na lafiya ba ne ganin cewa mijina dama ba ya gari.
Da dai suka ji babu wanda ya zo ya bude musu kofar sai suka balla kofar suka shigo gidan da karfin tsiya.Burum sai ga wadannan mutane a cikin falo dina sannan mu kuma mun kulle kan mu a cikin uwar daka.
Daya daga cikin su ya fasa gilashin windon uwar dakan sannan da ya hasko mu da fitilla sai yace mana ko mu bude ko kuma su harbe mu.
PT: Kina nufin cewa masu garkuwan sun shigo gidan ku da bindiga kenan?
Sumayya: Kwarai kuwa! Ganin wannan bindiga da suke rike da shi ne daya daga cikin ‘yan biyu ta tashi da sauri ta bude kofar uwar dakan sannan suka shigo.
Shigan su ke da wuya sai daya daga cikin su ya falle mini mari yace na bashi kudi. Ni kuma na ce babu kudi a dakin nan.
Nan da nan sai ya nuna min bindiga inda ya yi mun barazanar cewa idan ban basu kudi ba zai harbe ni. A firgice na dauko musu wani asusu da nake boye da shi na mika musu, suka fasa suka kwashi kudaden dake ci.
PT: Kina da masaniyyar adadin yawan kudin dake cikin asusun?
Sumayya: A gaskiya ba zan iya sanin ko nawa bane a asusun domin zubawa kawai nake yi.
Daga nan sai suka fito da mu waje inda na ga ashe suna da yawa sannan sun kuma kama wasu maza inda a cikin su akwai yaron abokin mahaifina mai suna Surajo.
A lokacin nan daga ni sai wata ‘yar fallen zane dake jikina kawai sannan a haka suka tattara mu tare da wadannan maza suka tafi da mu.
mun yi tafiyar kusan awa uku a kasa. Sannan da muka kai wani wuri sai suka hau babur da mu. Nan ma mun yi tafiyar awa daya da rabi.
Mun isa dajin da suka fara ajiye mu da karfe hudu na asuba.
A nan dajin mun yi tsawon makonni biyu sai masu garkuwan suka yi arangama da sojoji inda hakan ya sa suka kara shigewa da mu cikin daji.
A wannan dajin da muka koma mun yi tsawon makoni biyu kuma kafin suka sake dawowa da mu inda muka fara zama da farko a dajin.
Duk tafiyar da muke yi a kan babur ake dauke mu inda a dalilin haka na fara rashin lafiya.

PT: Ciwon me ya kama ki?
Sumayya: Ina ga a lokacin da aka kama ni ina dauke da ciki sannan yawan tafiya a babur kuma a daji ya kawo mun matsalar zuban jini. Haka dai na yi ta fama da wannan rashin lafiya na tsawon mako biyu.
Ya kai wani lokaci da har bana iya tafiya duk da haka wadannan mutane basu tausaya min ba sannan gashi tafiya ake yi babu tsaya wa.
Da wani cikinsu ya ga cewa ban iya tashi saboda ciwon da nake fama da shi sai ya tausaya min ya dauke ni ya dora a babur.
A dalilin ciwon da na yi har suma sai da na yi duk da haka wani ya yi mun barazanar ya kashe ni idan ban mike ba.
Da muka kai wani wuri a dajin sai muka ya dada zango sannan a nan ne na sami labarin cewa masu garkuwa sun karbi kudin fansan ‘yan biyu.
Nan da nan kuwa sai suka sake su ni kuwa aka bar ni tsakanin maza.
PT: Surajo fa?
Sumayya: Ina nan tare da Surajo a wannan daji sannan na ji labarin cewa maharan suka bukaci kudin diyan da ya kai Naira miliyan 30 a kai na da Surajo ko kuma su harbe shi.
Bayan wasu ‘yan kwanaki sai na ga an dauki Surajo an jefa shi cikin wata rami sannan aka harbe shi a kai.
A gani na masu garkuwan basu sami kudin da suke bukata bane ya sa suka aikata haka.
Na yi zaman wata daya a dajin bayan mutuwar Surajo sannan a lokacin ne na ji labarin cewa mutanen gidan mu sun ce za su biya kudin diyan Naira miliyan biyar a kai na.
PT: Tun da masu garkuwan suka sace ku wani irin abinci kuke ci?
Sumayya: Shinkafa suke bamu sannan nine ma nake girka wa in raba kowa ya ci.
PT: Cefane suke fita suke yi a waje ko kuwa suna tafe ne da kayan abincin?
Sumayya: Da kayan abincinsu suke tafiya sannan duk ranar da wani kayan hadin ya kare haka nan za mu ci abincin.
PT: Idan kin girka abincin har da masu tsaron naku kuke ci?
Sumayya: Eh wasu daga cikinsu ba amma kamar manyan basa cin wannan abinci da nake girkawa.
PT: A lokacin da kika fara rashin lafiya masu garkuwan sun baki magani ko ko kula?
Sumayya: A’a sai dai wani daga cikin su ne kawai ke bamu magani sannan shima din idan na hannun sa ya kare sai dai ka hakura.
PT: Yaya kika ji lokacin da maharani suka sake ki?
Sumayya: Da na dawo na taras a gida mutane na ta yi mun adu’o’I domin Allah ya sa a sake ni sannan mutane da dama sun zo yi wa iyaye na Allah kyauta. Da dama sai da suka yi kuka da suka gani.
Nima kai na ban tsammani zan iya dawo wa gida ba. Duk da haka ina wa Allah da mutane godiya. Allah ya saka da alkairi.
PT: Da kuka je asibiti likita ya tabbatar miki cewa cikin dake jikin ki na nan?
Sumayya: A’a yace na yi bari.
PT: Akwai abin da kike so duniya ta sani game da abin da ya faru dake a lokacin da kike hannun masu garkuwan?
Sumayya: I, ina rokon duniya da su ci gaba da yi wa mutanen da aka kama adu’a Allah ya sa a sake su su dawo gida lafiya domin kuwa a lokacin da nake daji mutanen da aka sace sun kai 27.
PT: Wani hukunci ne ki ka ga ya kamaci wadannan mutane dake sace mutane?
Sumayya: Allah dai ya shirya su kawai.
Discussion about this post