TASHIN HANKALI: Mahara sun far wa kauyukan Gusau, sun Kashe mutane 15

0

A tashin hankali da ya fada wa mutanen kauyukan Wonaka, Ajja, Mada, Ruwan Baure, Doka, Takoka da Tudun Maijatau ranar Litinin akalla mutane 26 ne suka rasa rayukan su inda da dama sun gudu da raunuka a jikin su.

Haka kuma Dakacin Gwashi dake karamar hukumar Bukuyyum ya kai karar irin wannan hari da ‘yan ta’addan suka kawo wannan yanki inda suka kashi mutane 11 duk a rana daya.

Basaraken ya kara da cewa bayan wannan hari da suka kawo, sun kone gidajen dake kauyukan gaba daya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun ceto wasu mata 6 daga hannun maharan da suka yi garkuwa da su.

Ya ce tuni dakarun ‘yan sanda sun far wa wadannan ‘yan bindiga da yanzu haka an sami dawowar zaman lafiya a jihar.

Shehu ya kara da cewa a binciken da suka gudanar sun gano cewa wasu fulani suka yi ramuwar gayya bisa kisan shanun su da kayi

A karshe yayi kira ga mutanen jihar da su guji daukar mataki a hannun su cewa gwamnati za ta hukunta duk wanda aka samu yana karya doka a jihar.

Share.

game da Author