Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta raba wa kananan ‘yan Kasuwa da talakawa akalla naira biliyan daya domin bunkasa sana’o’in su.
Wannnan tallafin da za a raba ba shi cikin Shirin gwamnati na raba naira biliyan biyu da dama can take da Shirin raba wa mutanen Jihar nan da kwanaki masu zuwa.
Tambuwal yace wannan tallafi na bashin Kudi za a ba mutane ne don su bunkasa sana’o’in su sanan babu riba ko ruwa a ciki. Abinda da aka baka shi zaka dawo dashi cikin shekara biyu ba daya ba.
Wannan taro ya samu halartar manya da kananan ‘Yan kasuwan Sokoto sannan kuma mutanen Jihar sun yabi gwamnan bisa wannan kokari da yake yi don kau da talauci da tallafa wa mutanen Jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan labari a shafinta ta yanar gizo.
Discussion about this post