TAMBAYA: Wa ye ya kashe jikan Manzon Allah Hussaini ( Radiyallahu Anhu) kuma a ina aka kashe shi?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Hakika azzalumai sun kashe Jikan Annabi SAW, Hussaini (RA), a cikin rikicin shugabanci da siyasa mai tsananin sarkakiya. Tarihin kashe
Hussaini (RA) yana da ruwayoyi da yawa masu matukar sarkakiya da dabaibayin siyasa tsakanin mabiya akidar Shi’a da kuma Ahlus Sunnah.
Dukkan bangarorin biyu sun ruwaito Kissosi mabambanta, akan wa ya kashe Hussaini (RA)? Da kuma abobuwan da suka faro har zuwa kisan da
bayan kisan.
A cikin wannan tambaya zan tsinto kadan daga cikin abinda na fahimta gwargwadon iko, bisa fahimta ta Ahlus Sunnah.
An kashe Hussaini (RA) ne a ranar Juma’a Hijira ta 61, a rana ta 10 ga watan Muharram, bayan ya kwana yana Sallah, a cikin wani yaki wanda a gwabza. An kashe Hussaini (RA) tare da Ahlul Baiti 18, kuma a yankin da ake kira da KARBALA da ke cikin kufa a kasar Iraqi ta yau.
Hussaini (RA) ya yi mutuwar shahada ne, kuma wadanda suka kashe shi sun aikata mummuna kuma mafi girman laifi, ba su kadaiba harma wanada ya basu gudun muwa, ko ya ji dadi, ko ya yarda da mugun aikin su. Kisan Hussaini (RA) abin takaici ne ga Musulmi, domin ka sancewarsa shugaba, daya daga cikin Malamai a cikin Sahabbai, Jikan Annabi SAW, mai matukan ibada ne da kyauta, kuma gwarzon jarimi ne.
To, wa ya kashe Hussaini (RA)? Akwai ra’ayoyi mabambanta akan haka:
1 – ‘Yan Shi’a suna zargin magabata daga cikin sahabbai akan kisan Hussaini (RA): kamar Mu’awiyya da Yazid da gwamnatin Banu Umayya.
2 – Amma Ahlus Sunnah kuwa sun tabbatar da cewa ‘Yan Shi’an Kufa ne suka kashe Hussaini (RA): an ruwaito cewa SHAMRU BIN ZIL JAUSHAN da
SANAN BIN ANAS ANNAKHA’I su ne suka kashe Hussaini (RA) kuma suka kuntule kansa karkashin umurnin Ubaidullahi Bin Ziyad (kuma sun kasance a cikin sojojin Sayyidina Aliyu (RA).
3 – Wasu mutanen Kufa su suka kashe Hussaini (RA): sun ki yin mubaya’ah ga Yazid, suka aikawa Hussaini (RA) da yazo Kufa za su yi masa
mubaya’ah, sai suka yaudaresa kuma suka kashe shi bayan kashe dan-uwansa Muslim Bin Aqil.
SHAHADAR HUSSAINI (RA) TA BAR BAYA DA KURA
1 – SHI’AH: ‘Yan Shi’ah suna wasu muyagun aiyyuka dangane da shahadar Hussaini (RA). Suna bikin tunawa da kisan Hussaini (RA) duk ranar
Ashura. Suna bayyana bakin ciki, kuka da kururuwa, dukan jiki, fasa jiki, sanya bakaken kaya, da fitar da jini a jikin su duk da sunan
ibada ko addini.
‘Yan Shi’a suna taro su gabatar da majilisi, wakoki, bayanai, da kasido, wadanda suke cin faskan magabata da zaginsu da tsinemusu da
dukkan wani batanci ga sahabbai batare da hakki ba. Suna karanto tasuniyoyi da labarai da kissoshin karya, kuma manufan wannan she ne
haddasa husuma, da rarrabuwan musulmai.
Hakan baya hallata kuma ba addini ba ne domin magabata basu yi haka ba. An hana Musulmi kukan mutuwa, da dukan jikinsa da fitar da jininsa
da duk wadannan Bidi’o’in da ‘Yan Shi’a suka kirkira.
Me yasa ‘Yan Shi’a ba za suyi koyi da manyan limaman su ba? ‘Ya’ya da jikokin wadannan da aka kashe, su basu aikata wadannan muyakun dabi’u ba.
2 – Wasu daga cikin Ahlus Sunna sun kirki wasu Bidi’o’in chika ciki, da murna da shagulgula da rabe-raden abinci da nama da dafe-dafe da
yanke-yanke da dinke-dinke da sunan addini ko ibada ranar Ashura.
Asalinsa shi ne kishiyantar ‘Yan Shi’a a lokacin da suke bidi’o’in bakin cikin tunawa da mutuwar Hussaini (RA), su kuma ‘yan sunnah suna
farin ciki da murna.
3 – ‘Yan-Shi’a n da ‘Yan sunnan duk sun kirkiro falala na karya akan haka. Abinda yafi dacewa shi ne mutun ya tsaya kan Al-Kur’ani da
Hadisi . Ka yi azumin Ashura kuma duk lokacin da katuna da wannan mummunan ta’addanci sai ka ce : Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
4 – Bukukuwan bakin ciki ko murna ranar Ashura be hallata ga musulmi ba. Tabbas wasu abobuwan sun faro a waccan lokaci, sakamakon siyasar bangarorin biyu. Amma jahilci ne kasa fahimtar haka a yanzu ga dukkan bangarorin.
Tambaya
1 – An kashe Sayyadi Hamza (RA) an farka cikinsa an yanki hantarsa an tauna an zubar, tare da cewar shima daya ne daga Ahlul Baiti. Me yasa ba a bikin bakin cikin ranar?
2 – Kakan Hussaini (RA) Fiyayyen Halitta, Annabin Rahama SAW ya yi wafati, tare da cewa ya fi Hussaini (RA) daraja. Me yasa ba a bikin
bakin cikin ranar?
3 An kashe Mahaifin Hussaini (RA) Sayyadi Aliyu (RA) ranar Juma’a a hanyarsa ta zuwa Sallar Asubahi, tare da cewar ya fi Hussaini (RA)
dara. Me yasa ba a bikin bakin cikin ranar?
Allah ka tsaremana Imaninmu da mutuncinmu. Amin.
Daga Imam Muhammad Bello Mai-Iyali