TA FADI GASASSA WA PDP: APC ba za ta yi takarar kowani kujera ba a Jihar Ribas – Kotun Koli

0

Idan ba a manta hukumar Zabe bata fitar da sunan Dan takara koda daya ba da sunan wai Dan takarar kujera ne a zabe mai zuwa a jam’iyyar APC.

Babban dalilin da ta bada kuwa shine har lokacin da aka rufe zaben fidda ‘yan takara na jam’iyyun kasar nan APC a Jihar ta gagara gudanar da zaben.

Jam’iyyar ta koma bisa hakan inda ta garzaya kotu domin a bi mata hakkin ta bisa wannan matsayi na hukumar zabe.

Nan da nan ta ko garzaya Kotun daukaka kara. Kotun ta yanke hukuncin cewa a yardar wa APC ta mika ‘sunaye Yan takaran ta sannan a tabbata an fafata da su a Zabe Mai zuwa.

A dalilin haka sai aka dunguma zuwa Kotun Koli domin a karkare ta a can.

Kotun Koli a ranar Juma’a ta yanke hukuncin cewa hukumar Zabe na da gaskiya a hukuncin da ta dauka na kin amincewa da ‘yan takara daga jam’iyyar APC.

Kotun ta yanke hukuncin cewa sai dai wasu jam’iyyun su fafata a Jihar Ribas din amma APC kada ta ko wulka a zaben Jihar tun daga na kujerun majalisar Tarayya da na jiha har zuwa na gwamna Jihar.

Share.

game da Author