Sultan da sarakunan Arewa sun halarci bude katafaren Masallacin Maiduguri

0

A ranar Juma’a ne sarkin musulmi Muhammadu Abubakar III tare da sarakunan yankin arewacin kasar nan 20 suka bude katafaren masallaci da dakin karatu a jihar Barno.

Shehun Barno ya bayyana wa sarakunan cewa wannan masallaci ya go Shekara 20 ana gina
shi. Aikin ya tsaya cak da sai da ya fara bi da kan sa yana neman taimako daga mutane.

Ya ce tun a wancan lokacin an kiyasta naira miliyan 800,000 ne za a kashe wajen yin wannan aiki.

A watan Yunin 2011 wani dan siyasa a jihar Kashim-Imam ya bada gudunmawar Naira miliyan 200 sannan gwamnatin jihar ta samar da sauran kudaden da ake bukata domin kammala ginin.

Sultan Abubakar ya jinjina wa Kashim-Imam, gwamnatin jihar da Shehun Barno kan kokarin da suka yi wajen ganin an kammala gina wannan masallaci sannan yayi kira ga mutanen jihar da suyi amfani da wannan masallaci da makaranta domin inganta addinin su da rayuwa.

A nashi tsokacin gwamnan jihar Kashim Shettima ya yi kira ga mutanen jihar da su maida hankali wajen neman ilimin adinin da na Boko.

Ya kuma ce gwamnatin sa ya gina makarantu da ya zuba kayan aiki na zamani da dama a jihar wanda yake saran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kadamar bayan zabe.

A karshe kwamishinan ilimi na jihar Mustafa Fannarambe ya bayyana cewa masallacin na da girman daukan mutane 10,000 a ciki sannan 5,000 a harabar masallacin.

Sannan masallacin na da dakunan karatu na darussan addinin,ruwan fanfo,janareto da sauran su.

Share.

game da Author