Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC Omoyele Sowore ya doke Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a mazabarsa dake jihar Ondo.
A sakamakon zaben da aka bayyana Sowore ya samu kuri’u 208, inda shi kuma Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 82, shi kuma Atiku na jam’iyyar PDP ya tashi da kuri’u 11.
Sowore ne dan takara na farko bayan Buhari da ya lashe mazabar sa a sakamakon zaben da ya bayyana zuwa yanzu.