Jami’an tsaro na sojoji da ‘yan sanda sun yi karin hasken tabbatar da kisan kiyashin da aka yi a wasu rugage a yankin kauyukan Karamar Hukumar Kajuru, cikin Jihar Kaduna.
Sojojin Najeriya sun ce mutane 66 ne aka kashe. Amma su kuma ‘yan sanda sun ce ba za su iya tantance adadin ba, sai dai sun yi karin bayanin cea sun kama mutane shida da ake zargi.
Wannan karin bayanin ya zo ne bayan an rika watsa suka da da tofin Allah-wadai kan sanarwar kisan mutanen da gwamnatin jihar Kaduna ta yi a ranar Juma’a, jajibirin zabe.
Gwamnan Jihar Kaduna ne, Nasir El-Rufai ya yi sanarwar ta bakin kakakin yada labaran sa, Samuel Aruwan, a ranar Juma’a.
A ranar Juma’a din gwamnatin jihar ta ce ta samu rahoto daga jami’an tsaro cewa an kashe mutane 66 a kauyukan da ke kewaye da Maro Gida da Iri a Karamar Hukumar Kajuru.
Wannan bayani takaitacce bai gamsar da jama’a ba, domin kowa ya dauka cewa a ranar Juma’ar ce aka yi kisan.
Hakan ya sa aka rika sukar gwamnan sosai, wasu ma na karyata cewa ba a yi kisan ba.
MASU KAKKAUSAR SUKA
Sai dai kuma da aka tsananta korafe-korafe, an gano cewa tun a ranakun Lahadi da Litinin da dare aka yi kashe-kashen, kwanaki hudu da biyar kafin gwamna ya bada sanarwa.
Yayin da wasu suka rika cewa ba gwamnatin jihar Kaduna ba ce ya kamata ta yi sanarwar, wasu kuma na ganin cewa me ya sa aka yi jinkirin bayyanawa har sai bayan kwana hudu.
Bayan kwana hudun ma sai a ranar jajibirin zabe?
CAN: Cikin wadanda suka yi wannan kakkausar suka har da Kungiyar Kiristoci ta Jihar Kaduna, CAN, wadda ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta yi kuskure da ta bada sanarwar ana gobe zabe. Ta ce ba lokaci ba ne da za a yi irin wannan sanarwa mai tayar da hankulan jama’a, a daidai lokacin da za fara jefa kuri’a.
SOKAPU: Haka ita ma Kungiyar Kare Muradun Kudancin Kaduna (SOKAPU), kira ta yi ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da Daraktan SSS na Kasa su kafa kwamitin bincike mai zaman kan sa domin a binciko hakikanin abin da ya faru dangane da zargin wannan kisan kiyashi.
Kakakin Yada Labaran kungiyar, Yakubu Kuzamani, ya ce abin al’ajabi ne a ce gwamna ne da kan sa ya yi wa jama’a bayanin wadanda aka kashe din ba jami’an tsaro ba.
SHEHU SANI: Shi ma Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce Gwamna El-Rufai ya yi karin gishiri wajen bayyana adadin wadanda aka kashe. Kajuru na cikin mazabar Kaduna ta Tsakiya ce, inda Shehu Sani ke wakilta.
Ya ce wadanda aka kashe din ba su wuce 10 zuwa 15 ba, kuma tun ranakun Lahadi da Litinin aka yi kashe-kashen. Sannan kuma gwamnati ta kara yawan wadanda aka kashe.
Daga nan ya ce lokacin da gwamnan ya yi sanarwar, ba lokaci ne da ya dace a yi sanarwar ba. Ya ce cikin kunkuzunn daji ne rikicin ya barke, inda akasarin ‘yan jarida ba su iya shiga wurin domin su gane wa idon su.
Shehu ya ce da gayyar siyasa gwamna ya yi jinkirin bayyana labarin, har sai da ya bari ana gobe zabe, domin cimma wani mummunan burin sa na siyasa.
CHIDI ODINKALU: Jinkirin bayyana kisan sai bayan kwana hudu, ya sa da dama jama’a sun rika tababar yin kisan kiyashin, domin ba su ji labarin an yi kashe-kashe a ranar jajibirin zabe, ranar da aka yi sanarwar ba.
Irin hakan ce ta sa tsohon Shugaban Hukumar Kare Hakkin Dan Adam, Chidi Odinkalu, wanda kuma abokin Gwamna El-Rufai ne, ya shiga gidan talbijin na Channels ya ce ya kasa tabbatar da hakikanin kisan wanda gwamna ya yi sanarwar cewa an yi. Ya ce ya tuntubi majiya da dama.
Ra’ayin sa ya fi karkata cewa mugayen ‘yan siyasa ne suka fito da rahoton a daidai lokacin da za a fara zabe, domin su kawo dalilin da zai sa a dage zabe a kasar nan.
GANI DA IDO: A ranar Asabar da ta gabata sai gwamna El-Rufai da kan sa tare da rakiyar Kwamandar Rundunar Sojan Najeriya ta 1 da ke Kaduna, Kwamishinan ‘Yan Sanda da Shugaaban SSS na Jihar suka kai ziyara har cikin rugagen da aka yi kashe-kashen.
KISAN YANKAN-RAGO: A yayin ziyarar ce aka nuno wani bidiyo inda Kwamandan Sojojin Farouk Yahaya ke bayanin irin munin da kashe-kashe da koken su ka yi. Ya ce mutane 66 aka kashe, 37 daga cikin su kuwa gefen kogi aka kai su aka rika yi musu yankan-rago.
“A lokacin da labarin ya zo gare mu, sojojin mu sun je tare da jama’ar kauyukan domin su tantance irin munin da barnar ta yi. Mun nuna muku wancan yankin a cikin kauyen. A can ne aka ba mu labarin cewa an tafi da su aka rika yi musu yankan-rago a bakin rafi.” Inji Manjo Jamar Farouk Yahaya.
“Mutane 37 aka yi wa yankan-rago a can bakin rafi. Ramin da aka rufe su kuma ya na can. Kun ma dai ga kabarin na su a can, kuma kun ga irin tufafin su da kuma jinin da ku ka rika gani. A can haka kuma ku na kallon rugagen su da aka babbanka wa wuta.
Ya kara da cewa saboda Fulanin ba a wuri daya suke ba. An rika bin matsugunan su nan da can ana konewa bayan an karkashe su. Ya ce cikakken bayanin da ya je musu kenan.
A cikin bidiyon za a iya ganin El-Rufai na tambayar kwamandan adadin mutanen da aka kashe. Inda ya ce masa su 66 ne aka kashe. Yayin da shi kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda ya ce masa sun kama mutane shida.
RUGAJE TAKWAS DA AKA YI KISA DA YANKAN RAGO
PREMIUM TIMES ta samu karin cikakkun bayanan da suka tabbatar da cewa an kashe mutane 66 a Karamar Hukumar Kajuru, kamar yadda Gwmnatin Jihar Kaduna ta bada sanarwa.
An kai harin ne tun ranar Litinin, kuma hari ne na ramuwa, wanda aka kai wa wasu can baya.
Wannnan karin bayani ya fito fili ne bayan da aka rika waswasin cikakken abin da ya faeru.
Gwamna Nasir El-Rufai ne ya bayyana cewa an jami’an tsaro sun ba shi rahoton samun gawarwaki har 66, kuma ya yi sanarwar a jribirin zabe.
Wannan dalili ne ya sa mutane da yawa suka dauka cewa a ranar Juma’a din aka yi rikicin.
Gwamnan ya ce wasu batagari ne suka kashe su, yayin da suka kai musu hari a yankunan Maro Gida Iri, cikin Karamar Hukumar Kajuru.
Ya ce rugagen da kisan ya faru a cikin su, sun hada da: Rugar Bahago, Rugar Daku, Rugar Ori, Rugar Haruna, Rugar Yukka Abubakar, Rugar Duni Kadiri, Rugar Shewuka da Rugar Shuaibu Yau, inji shi.
Sai dai kuma gwamnan bai bayyana jami’an tsaron da suka ba shi rahoton kisan ba.
Chidi Odiankalu na Hukuamr Kare ‘Yancin Dan Adam da jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna duk sun yi tababar kisan, saboda babu wani sahihin karin bayani daga bangaren gwmnati.
Amma kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa El-Rufai ya yi wannan jawabi ne bisa rahoton da Operation Yaki suka bas hi a sirrrance.
Oeration Yaki ya kunshi ‘yan sanda, Sojiji da kuma SSS.
Rahoton jami’an Operation Yaki da suka raka wasu Fulani cikin rugagen su, sun samu gawarwaki har 66, ciki har da na kananan yara 22 da mata 12.
Wakilin PREMIUM TIMES a jihar ya zanta da wasu.
Benjamin Maigari, wanda ya ce ya je yankin ne domin ya yi zabe. Ya ce an kai hare-hare ne guda biyu. Na farko kabilar Adara ne aka kai wa harin. Na biyu kuma harin ramuwar gayya ne a kan Fulanin.
Sai dai kuma ya ce harin ramuwar gayyar shi ne ya fi cin rayuka da dama.
Ya ce harin da aka kai wa kabilar Adara a ya ci rayuka 11 tun a ranar Litinin.
Ya kara da cewa su kuma kabilar Adara sun yi zargin cewa Fulani ne suka kai musu hari, sai kawai suka tashi a cikin daren suka shiga kashe Fulani a cikin rugagen su.
“Harin da aka kai wa Adara an kashe mata da kananan yara. Haka na Fulanin an kashe mata da kananan yara da dawa.”
Ya ce jami’an ‘yan sanda sun je a washegari, domin su tantance irin barnar da aka yi. Sun gana da Hakimin Kajuru da kuma DPO na Karamar Hukumar Kajuru.
Discussion about this post