Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka kan yadda Daloli da kudaden Kasashen wake suka karade kasar nan a dan Kwanakin nan.
Buhari yace yaduwar wadannan kudade a kasarnan a daidai lokacin Zabe da muke ciki makirci ne da wasu suka shirya domin su siya kuri’u daga hannun mutane ko da karfin arzikin su.
Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ne ya bayyana haka da yake karanta sakon shugaban kasa bayan ganawar majalisar kasa na mako-mako da aka yi ranar Laraba.
Buhari ya bayyana cewa tuni har ya umarci hukumar EFCC da ta bi diddigin watsuwar wadannan kudade sannan a taso keyar duk wadanda suke raba irin wadannan kudade.
Bayan haka ya yabawa hukumar bisa kokarin da tayi na bibiyar kafafen da wadannan kudade suka fito har ya shiga hannun mutane.
Discussion about this post