Sirikin Ganduje, Gwamna Ajimobi ya karbi kaddarar rashin kujerar sanata

0

Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi, ya bada sanarwar karbar kaddadar faduwa zaben neman kujerar sanata da ya yi mai da zai wakilci Shiyyar Oyo ta Kudu.

A cikin wata sanarwa da kakakin yada labaran sa, Bolaji Tunji ya bayar, Ajimobi ya taya dan takarar PDP Kola Balogun murnar kayar da shi da ya yi.

Balogun dai ya kayar da Gwamna Ajimobi da ratar kuri’u 13,502.

Yayin da PDP ta samu kuri’u 105,720, ita kuma APC da ta tasaida gwamnan na Oyo a matsayin dan takarar ta, ta samu kuri’u 92,217.

An yi wannan sanarwar jiya Litinin daga bakin jami’in INEC mai fadar sakamakon zabe, Wole Akintola cewa Ajimobi ya fadi a kananan hukumomi dukkan hudu da aka fara bayyawa.

Ajimobi ya ci kananan hukumomi uku, shi kuma Balogun ya ci shida.

Share.

game da Author