Shugabar mata ta fallasa aringizon kuri’u a mazabar Oshiomhole

0

Wata shugabar matan jamiyya mai suna Abibat Momudu, ta kutsa kai cikin dakin da ake tattara sakamakon zabe ta na hargowar cewa an yi aringizon kuri’u a mazabar ta da ta Adams Oshimhole, shugaban APC na kasa.

Hakan kuwa ta faru ne a Mazaba ta 2, da ke karkashin Karamar Hukumar Etsako, Auchi, a jihar Edo.

Ka kai korafin ne da karfe 6:47 na yammacin ranar Asabar, inda ta ke kukan cewa an yi aringizon kuri’u a mazabar ta da ta Oshimhole.
A nan take Abibat ta nemi a soke zaben da aka yi a akwatinan mazabar ta da ta Oshiomhole.

A hirar da matar ta yi da PREMIUM TIMES, ta tabbatar da cewa an dauke kuri’u 700 daga runfar zaben da ta ke, an yi amfani da 300 kacal.

Ta ci gaba da cewa, da ta yi magana sai jami’in zaben wurin mai suna Udo Udodo da kuma dan sandan da ke kula da wurin suka ce kawai ta manta kada tsaya wani bincike, a wuce wurin kawai.

Abibat ta ce amma sai ta ki yarda, ta ce ba ta yarda kowa ya sa hannu ba kan sakamakon zaben a wannan mazabar.

Ta ce ta rubuta korafi a rubuce ta kai, kuma ta na da yakinin cewa za a duba kukan na ta.

PREMIUM TIMES dai ta kawo muku labarin yadda APC ta yi nasara a akwatinan rumfar zaben mazabar sa.

Share.

game da Author