Shugabar Kotun Daukaka Kara, Zainab Bulkachuwa, ta hori kotunan da ke sauraren kararrakin zabe da cewa kada su rika yawan daga kararrakin zabe domin kawai a rika haifar da jan-kafa da bata lokacin maras dalili.
Ta bayar da wannan shawara ne a yayin da ta ke jawabi wurin taron bayar da horo ga alkalan da za su saurari kararrakin zabe na 2019 mai zuwa a karshen wannan makon.
Ana gudanar da taron ne a Abuja. Ta ce tilas ne su rika gudanar da ayyukan so a kan turbar doka da kuma bisa cika alkawarin rantsuwar da suka yi kafin a dauke su aikin.
“A yanzu fannin shari’a na Najeriya ya na kan wani siradi ne. Ya zama wajibi mu yi aikin mu kamar yadda dokar kasa ta tanadar a cikin tsarin da da bai kauce wa shari’a ba.
“Mu yi aikin mu ba da tsoro ko nuna bambanci ba, ko kuma kullatar wani. Domin akwai rantsuwa a kan mu kafin mu fara wannan aikin.
“Sannan ina so na tunatar da ku cewa dukkan ku akwai jami’an da ke sa ido su na kallon duk abin da za ku aikata. Saboda ba zai sassauta wa dukn wani da aka kama ya aikata harkalla ko ya yanke hukuncin da ya kauce wa abin da dokar kasa ta gindaya.”
“Ku kasance ku ne ke iko da kotun ku, kada ku bari son rai, kaunar wani, tausayin wani ko kullatar wani ya fizge ku har ku ba mai gaskiya rashin gaskiya, ko kuma ku bayar da gaskiya ga maras gaskiya.” Inji Bulkachuwa.
Discussion about this post