Sharrin Madigo A Cikin Al’ummah
Bismillahir Rahmanir Rahim
Yaku bayin Allah! Ku sani, lallai ‘yan luwadi da ‘yan madigo sun kauce wa dabi’ar da Allah ya halicci ‘yan Adam a kan ta (wato fitrah), ta hanyar mace da namiji su auri juna su ji dadin junansu, kuma su samar da zuri’ah dayyaba, wadda Annabi (SAW) zai yi alfahari da ita. Kai ko dabbobi ma basa yin abinda ‘yan luwadi da ‘yan madigo suke yi, na mace-ta-nemi-mace, namiji-ya-nemi-namiji.
Don haka duk wanda kuka ga ya kauce wa dabi’ar da Allah ya halicce shi a kan ta, ya fada wata hanya da ba ta dace ba, ta madigo da luwadi, to lallai dabbobi ma sun fishi tunani da hankali. Sannan suna cikin masu haifar da musibu a cikin al’ummah.
Yaduwar luwadi da madigo a cikin al’ummah ya jawo karin yaduwar cututtuka masu wahalar warkarwa, kamar cutar AIDS, da yake karya garkuwar jikin Dan Adam, da sauran cututtuka masu hadarin gaske ga lafiyar ‘yan Adam.
Wadannan miyagun dabi’u suna jawo matsalar zamantakewar iyali, suna jawo kasala da ragwanci a cikin al’ummah, har a wayi gari al’ummah ta zama sokuwar al’ummah da sauran al’ummomi suka yiwa fintinkau. Suna jawowa al’ummah karin jahilci da yin watsi da harkar ilimi da ilimantarwa.
Kai ko da ace luwadi da madigo basu haifar da wata illa a cikin al’ummah, ya zama wajibi Musulmi ya nisance su, tun da mahaliccinsa ya hana. Kuma muna sane da cewa, duk abunda Allah ya hana toh wallahi barin sa alkhairi ne a gare mu, aikata shi kuwa sharri ne da zai iya rusa zaman lafiyar al’ummah da ci gaban ta.
Imam Ibnil Qayyim Al-jawziyyah yana cewa:
“Zina, luwadi da madigo suna tattare da zubewar mutunci da wulakanta, da suke sa mutum ya kaucewa manufar Allah a kan sa. Kuma sun kasance manya-manyan zunubai abin kyama a wurin Allah. Sannan suna tattare da sharri da cutar da ta kai ace mutum ya rasa rayuwar sa ta hanyar kisa da ace an aikata wannan a kan sa. Saboda duk mutumin da ya dauki wannan hanya ta lalacewa, to ya zama sharri da guba a cikin al’ummah. Za’a wayi gari baya jin kunyar Allah baya jin kunyar mutane. Kuma shiriya za ta yi wahala a wurin irin wannan mutum, sai fa idan Allah ne ya nufe shi da shiriya. Maniyin da aka zuba wa mutum a jikinsa ta hanyar zina, madigo ko luwadi, guba ne a cikin jikinsa kuma dafi ne mai cutarwa. Shi yasa malamai suka yi sabani shin mai aikata irin wannan aiki zai shiga Aljannah kuwa? Akwai maganganun malamai guda biyu kamar yadda Ibn Taimiyyah ya fada.” [Duba Jawabul Kaafi, shafi na 115]
Madigo shine mace ta nemi mace ‘yar uwarta, domin taji dadi da ita, ta gamsar da ita ta yadda namiji zai gamsar da ita.
Madigo wanda a turance ake kira da lesbianism yana nufin saduwa ta hanyar gogayya tsakanin mace da mace ta amfani da halittarsu, domin kau da sha’awar junan su. Idan wannan ya kasance a tsakanin namiji da namiji to ya koma luwadi kenan. Wal iyazu billah!
Neman jinsi ya faro ne tun daga zamanin Annabi Lut (AS). Wanda tarihi ya nuna cewa shaidan ne yazo a cikin siffar ‘yan Adam, ya nuna wa mutanen Annabi Lut (AS) yadda zasu rinka neman junan su.
A yau, an wayi gari duniyar kimiya da fasaha musamman duniyar yanar gizo (internet), na daya daga cikin hanyoyin da ke koyar da wadannan munanan dabi’u, musamman a social media, inda zaka tarar a can da suna yi a boye, yanzu kuwa sun fito fili har groups su ke da shi daban-daban a Facebook, WhatsApp da sauran su. Wani abin takaici shine, sai ka tarar mafi yawansu duka hausawa ne, musulmai, ‘yan arewa. Sharrin yahudawa ne, kuma sannu a hankali suna samun nasara.
Madigo wata mummunar dabi’a ce da ko dabbobi basa neman junansu, amma sai gashi ta bayyana ga ‘yan Adam. Allah ya la’anci mai yin ta. Kuma wanda duk Allah ya la’ana to wallahi babu shi babu albarka a rayuwar shi. Kuma babu shi babu samun alkhairin duniya da na lahira.
Yaku bayin Allah! Mala’iku suna da hankali amma basu da sha’awa. Mutane suna da sha’awa kuma suna da hankali. Su kuwa dabbobi suna da sha’awa amma basu da hankali. Anan, a duk lokacin da hankalin dan Adam ya rinjayi sha’awarsa to sai ya koma daga cikin mala’iku, domin su ke da hankali amma basu da sha’awa. Idan kuwa sha’awar Dan Adam ta rinjayi hankalin sa to sai ya koma daga cikin dabbobi, domin sune ke da sha’awa amma basu da hankali.
Madigo musiba ce ta shigo cikin al’ummah wadda zata iya haddasa kowane irin fushin Ubangiji. A yau bala’o’in da muke ji suna faruwa a wasu kasashen waje, na girgizar kasa, iska da tsawa gami da kashe-kashe da yake-yake da zubar da jini babu kakkautawa, gasu nan biye da mu, ba domin komai ba, sai don wadannan miyagun ayyukka da ke gudana a cikin al’ummah.
Ta fannin zamantakewa da kiwon lafiya kuwa, hakika akwai illoli masu yawa da madigo ke haifarwa a jiki kamar haka:
1. Yana kauda sha’awar aure baki daya. Domin a addinance akan daura aure tsakanin mace da namiji. To macen da take madigo zata kasance bata shawar namiji baki daya. Ko tayi auren, tayi ne kawai, amma ba zata yi shawar mijin ta ba.
2. Ba zata sami biyan bukata a kwanciyar aure ba. Shi kuma jima’i a tsakanin ma’aurata, yana kara gina so da kauna a tsakanin juna. Koda an sadu da ita, to ba zata ji shawarta ta gushe ba har sai ta hadu da ‘yar uwarta mace sun goga da juna. Shi yasa kake ganin matan aure na aikata wannan mummunar dabi’ar.
3. Madigo na haifar da yaduwar ciwon sanyi. A duk lokacin da wadda take dauke da ciwon sanyi tayi tarayya da wadda bata da shi, to anan zai yadu. Domin wannan discharge din yana dauke da kwayoyin cuta da zai yadu ya shafe ta.
4. Madigo yana haifar da cututtukan da ke sa kaikayi ga farjin mata. Idan mai kaikayin mara ko kuraje a cikin farji ko zubar farin ruwa, sanadiyyar wani infection, kamar na vulvo vaginal candidiasis, yeast infection, da sauran su, idan suka yi gogayya da juna, to zata dauki wannan ciwon.
5. Madigo yana haifar da yaduwar cutar sida (AIDS). Kuma ban ga yadda za’a kare wannan kwayar cutar ba, domin takan biyo ruwan dake fitowa a gaban mace ta shafi ‘yar uwarta, kuma ba za’a iya amfani da condom ba, kuma ma bincike ya nuna cewa Condom ba ta iya kare komai. Kawai magani shine, aji tsoron Allah a daina.
6. Madigo yana haifar da ciwon mara – Dama, su mata sun fi kowa yawan ciwon mara, wasu ma dai dashi aka haife su, wasu kuma a lokacin al’ada yake zo masu, wasu kuma daga baya suka dauko shi a wani wuri (infections). Gogayyar da suke yi gaba da gaba da juna na haifar da kamuwa da ciwon mara, musamman na infections. Ayi ta faman neman magani a rasa sanin dalili.
7. Madigo yana haifar da ciwon ruhi – Anan shi ciwon ruhi ba fa ciwo bane da zaki gani a zahiri, amma a hakika zaki ji alamunsa a gangar jikin ki. Na farko dai zai busar da zuciyar ki, sai ya kasance baki shakku ko tinanin zaki iya mutuwa a kowane lokaci.
Sha’awarki zata gushe ta koma ga ‘yan mata kawai. Da zaran kin ga mace mai girman kirji ko mai manyan duwawu duk sai sha’awarta ta kama ki.
Komai nisan ki da ita zaki iya neman ta. Har ki tsufa zaki kasance kina ganin sha’awar mata ‘yan uwanki.
8. Sirrance zai janyo maki gushewar farin jini a fuskar maza, sai kiga duk masoyanki mata ne, gaki kyakkyawa amma bamai so, basirar ki tabi ta dushe, tunanin ki ya sauya. Wata rana sai ki kasa daina wa. Kuma zuwa gaba sai ya busar da ke, ki rinka ramewa, duk ni’imar jikin ki ta mace, ta gushe, kibi ki bushe, kiyi matukar muni. Kuma a lokacin sai kiyi dana-sani, a lokacin da dana-sanin ba zai amfane ki ba! Allah ya shirye mu baki daya, amin.
Wassalamu Alaikum
Dan uwan ku:
Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Nijeriya. Za’a iya samun Imam ta adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.