Shugaban cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Barno Sule Mele ya bayyana cewa amfani da mutanen da suka san gari ya taimaka wajen dakile yaduwar cutar shan-inna a jihar.
Ya ce a dalilin amfani da mutane irin haka ya sa cibiyar su ta gano yara 17 dake dauke da cutar da kuma yaran dake bukatan allurar rigakafi a wasu bangarorin jihar dake da wahalan shiga.
Mele ya ce hukumar su za ta horas da mutane game da irin haka domin samun nasara wajen kawar da cututtukan dake kisan yara kanana a jihar.
Jami’in kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Clement Peter ya jinjina amfani da wannan dabara da fannin kiwon lafiyar jihar Barno ta yi.
Ya ce haka zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar yara kanana da mata dake zama a wasu sassan Najeriya da ma’aikatan kiwon lafiya ba su iya zuwa.
Bincike ya nuna cewa Najeriya, Afghanistan da Pakistan na daga cikin kasashen duniyan da har yanzu ke fama da cutar shan-inna a kasashen su.
WHO ta ce hakan na da nasaba ne da rashin mai da hankali wajen yi wa yara allurar rigakafi musamman a wasu sassan kasar nan dake da wahalar shiga musammam saboda tashe-tashen hankula.
Discussion about this post