‘Yan Kasuwar Gumi daker Kaduna sun tashi cikin taashin hankali da juyayin hasarar da suka tafka a sanadiyyar gobara da aka yi a kasuwar cikin daren Talata.
Wannan gobara sai da ya lashe shaguna 31 da masallacin dake Kasuwar ta bangaren da aka fi sani da bakin Dogo.
Wasu masu gadin masallaci dake cikin kasuwan sun bayyana wa wakilan jaridu cewa akwai tabbacin wutan lantarki ne ya yi sanadiyyar tashin gobarar.
” Mun yi kokarin tada mutane daga barci domin su kawo mana taimako amma hakan bai sa an dace da kashe wutan ba. Sannan su kan su masu kashe gobara da kyar suka yi sa’an kashe wannan wuta.
Shugaban kungiyar masu injin nika rogo a kasuwan Alfa Hussaini ya tabbatar da haka inda yake kira ga gwamnati da ta kawo musu agaji a kasuwar.
” An yi hasaran dukiya na miliyoyin naira sanadiyyar wannan gobara sannan mafi yawan shagunan da suka kone na mata ne masu injin nika rogo dake neman taro-sisi.
Wani tsoho da shagon sa a kone a kasuwar ya yabawa hukumar kashe gobara bisa kokarin da tayi wajen kashe gobarar duk da dai an yi hasara matuka. Sannan ya roki gwamnati da ta taimakwa mutanen da wannan gobara ya shafa cewa a agaza musu domin kusan dukkan su marasa karfine ba wani jarin kirki suke da shi ba.