Jam’iyyar SDP mai alamar doki ta kori Jerry Gana daga Jam’iyyar tare da dakatar da Donald Duke. Sannan shi ma wani jigon SDP din mai suna Dipo Sonibare, an dakatar da shi.
Wannan rikicin jam’iyya ya kunno kai ne na baya-bayan nan, tun bayan sanarwar da jam’iyyar ta yi cewa magoya bayan ta su zabi Buhari, dan takarar shugaban kasa a karkashin APC.
SDP ta ce ta yanke shawarar cewa Buhari za su zaba ganin yadda rikicin fito da halastaccen dan takarar shugaban kasa na SDP din ya ki ci, ya ki cinyewa.
Jerry Gana ne shi da Donald Duke ke ta dambarwar neman halascin takarar a kotu. Idan wannan kotu ta halasta wa wancan a yau, a gobe kuwa sai wata kotun ta halasta wa dayan.
A yanzu dai tsohon ministan ilmi, Tunde Adeniran shugaban riko na SDP. Sai dai shi ma din ya na from fuskantar tawaye daga wani bangaren magoya bayan jam’iyyar.
Mataimakin Shugaban SDP na riko, Olu Agunloye ne ya fitar da sanarwar dakatarwar.
Idan ba a manta ba Kotun Daukaka Kara a Abuja, ta tsige Jerry Gana, ta maida na farko, wato Donald Duke a matsayin dan takarar shugaban kasa na SDP din.
Tun da farko dai Duke din ne ya ci zabe da kuri’a 812, shi kuma Gana ya samu kuri’a 611.
A ranar 4 Ga Disamba, 2018 ne Mai Shari’a Hussein Baba-Yusuf ya cire Duke ya maye shi da Gana, wanda ya kai kara ya ce bai yarda da tsaida Duke ba.
Baba-Yusuf ya kafa hujja da cewa ka’idar jam’iyyar SDP ta nuna cewa dan takarar shugaban kasa ba zai fito daga shiyya daya da shugaban jam’iyya ba.
Wannan ne ya sa Baba-Yusuf ya ce wa SDP da INEC Gana ne halastaccen dan takara.
Su kuma shugabannin jam’iyya suka garzaya Kotun Daukaka Kara, domin rashin amincewa da hukuncin Babbar Kotun Tarayya.