‘Yan Najeriya sun fita jefa kuri’ar zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya a ranar 23 Ga Fabrairu, 2019. Bayan nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya sake samu, an zabi sanatoci 109 da za su je Majalisar Dattawa da kuma mambobin Majalisar Tarayya 360.
Wadanda aka zaba din kuwa za su kasance su ne zubin ‘yan majalisar na 9 tun bayan fara dimokradiyya a Najeriya. Su ne kuma za suma ye gurbin zubin majalisa na 8 da za su sauka a ranar 29 Ga Mayu, 2019.
Za a dade ana tuna wannan zubin majalisar dattawa da ke kai a yanzu, musamman dambarwa, kwatagwangwama, rudani, rincimi, kakuduba, tuggu, zagon-kasa, kutungwila da algungumancin da aka rika yi a tsakanin Shugaban Majalisar na yanzu, Bukola Saraki da kuma bangaren gudanarwar Gwamnatin Tarayya da kuma APC, jam’iyyar da ya taimaka, ya kafa ta kafa mulki.
Ba a taba yin shugaban majalisar dattawa wanda ya shafe wa’adin sa cikin kandamin ruwan rikici kuma ya kammala zangon sa ba, sai Saraki.
RUFE DAKI DA ‘BARAWO’ A CIKI
Rundunar sanatoci 109 da aka zaba a ranar Asabar da ta gabata, ba za su bambanta da wadanda za su sauka a yanzu ba. Akwai wadanda za su yi kome, sannan kuma akwai wadanda sabbin-yanka-rake ne, wannan ne zuwan da za su yi na farko.
A cikin su kuma akwai gogaggun ‘yan siyasar da har gwamna sun taba yi tsawon shekaru takwas.
Sannan kuma akwai akalla 11 daga cikin su, wadanda ake zargi, kuma ake kan shari’ar zargin satar kudin al’umma da suka yi, amma duk da haka talakawa suka zabe su domin su wakilce su a majalisa.
PREMIUM TIMES ta yi nazarin wasu sanatocin da aka zaba alhalin gwamnati na zargin su na danyen kashin da zai addabi zauren Majalisar Dattawa da wari.
Sanatocin dai duk da harkallar da ke tattare da su, talakawa sun zabe su a matsayin manyan shiyyoyin su a zauren majalisa, kuma manyan shiyyoyin su a jiha da karkarar su.
ORJI UZOR KALU
Tsohon Gwamnan Jihar Abia ne, kuma an zabe shi Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC.
Shekara da shekaru EFCC ta gurfanar da shi kotu bisa zargin satar kudin jihar Abia. Shi da kamfanin sa mai suna Slok Nigeria Ltd da kuwa Ude Udeogo ake kara. Udeogo shi ya yi wa Kalu Kwamishinan Kudi a zamanin da ya yi gwamna.
Ana neman naira bilyan 7.7 a hannun Kalu. Tun bayan kammala wa’adin sa na gwamna cikin 2007 aka fara shari’a da shi. daga baya shari’ar ta shiririce, sai cikin 2016 bayan Buhari ya hau mulki aka kakkabe fayil din shari’ar aka ci gaba.
Kalu ya tuma tsalle ya koma APC bayan an ci gaba da shari’ar sa. Shari’ar ta dauki sabon salo cikin watan Nuwamba, bayan da ya fice daga kasar nan ba tare da sanin alkalin da shari’ar ke hannun sa ba.
Mai Shari’a ya bada umarnin da ya shigo Najeriya a kama shi. bayan ya dawo, maimakon a ji cewa an cafke shi, sai aka ji Kalu ya bulla a jihar Abia ya na ta kamfen na neman sanata a karkashin APC. Kuma ya yi nasara.
GABRIEL SUSWAM
Shi ma tsohon gwamna ne a jihar Benuwai da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP domin ya wakilci mazabar Benuwai ta Arewa.
Ana tuhumar sa za wawure naira biliyan 9.1, shi da wanda ya yi masa kwamishinan kudade da akantar jihar ta lokacin, mai suna Janet Aluga. Akwai tuhumomi 32 a kan su.
EFCC ta ce an sace kudaden tsakanin 2012 zuwa 2015.
CHIMAROKE NNAMANI
Nnamani ya taba yin gwamna a jihar Enugu, kuma a yanzu sanatan PDP ne da zai wakilci mazabar Enugu ta Gabas.
Shi ma shari’ar sa ta jima, domin tun cikin 2007 bayan ya sauka daga gwamna aka maka shi kotu a bisa zargin shi da wani hadimin sa mai suna Sunday Anyaogu da wasu mutane shida, sun hada baki sun sace naira bilyan 5.3 daga kudaden jihar Enugu.
An yi ta yin ’yar-gala-gala da shari’ar, daga wannan alkali zuwa wannan mai shari’a har kotuna uku.
Cikin watan Fabrairu, 2018 ne wata Babbar Kotu a Lagos ta kori karar bisa dalilin EFCC ta kasa gabatar da shaidun da za a iya amfani da su cewa Nnamani ya ci kudin har a daure shi.
Tun a lokacin dai EFCC ta ce za ta daukaka kara, domin ba ta gamsu da hukuncin da mai shari’ar ya yanke ba.
IFEANYI UBAH
Ifeanyi Ubah ya ci sanatan Anambra ta Kudu a karkashin jam’iyyar YPP. Ya kayar da abokin karawar sa Andy Uba na jam’iyyar PDP.
EFCC na bincikar sa kuma ta gurfanar da shi kotu saboda zargin hadin baki ya damfari gwamnatin tarayya naira bilyan 43.29 da kamfanin sa Capital Oil and Gas Limited ya yi na kudin tallafin man fetur, wato ‘petroleum subsidy.’
EFCC ta ce ya rika bin hanyar fojare, harkalla, murda-murda da asarkala ya karbi kudin a hannun gwamnati a cikin 2011.
PETER NWAOBOSHI
INEC ta bayyana Peter Nwaoboshi matsayin sanatan da ya lashe zaben Jihar Delta ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC.
Cikinn watan Afrilu, 2018 ne EFCC ta maka shin kotu bayan ta cafke shi a bisa zarfin shi da kamfanonin sa biyu da tafka zambar naira milyan 322.
Mai Shari’a Mohammed Idris ya tura shi kurkuku, amma bayan kwana biyu kacal aka bada belin sa.
ABBA MORO
Abba Moro ya yi Ministan Harkokin Cikin Gida a zamanin mulkin Goodluck Jonathan. A yanzu shi ne zababben sanata mai wakiltar Benuwai ta Kudu da aka zaba a karkashin PDP.
Moro ya kayar da fitaccen dan siyasa Stephen Lawali wanda ya wakilci APC.
A zamanin Abba Moro na ministan harkokin cikin gida ne suka shirya gangamin atisayen gwajin daukar matasa aikin jami’an shige da fice, wanda aka gudanar a filayen kwallon fadin kasar nan.
Cincirindon jama’ar da suka halarta ya jawo mummunar tirmitsitsi har aka yi asarar rayuka 20.
Daga baya kuma EFCC ta zagi Abba Moro da gada-gada da kuma daka-dakar cinye dala milyan 2.5 na kudaden sayen fam da matasan suka biya, domin neman a dauke su aiki.
Maganar na kotu har yanzu, Moro kuma ya ce shi dai bai karkatar da ko sisi ba.
STELLA ODUAH
Stella Oduah ta yi MinistarHarkokin Sufurin Jirage a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan. Dama a yanzu haka sanata ce a karkashin PDP, kuma aka sake zaben ta a wannan zango da aka yi zabe ranar Asabar, 2 Ga Fabrairu.
Oduah za ta ci gaba da wakilcin Anabra ta Arewa.
Tun bayan saukar ta ake zargin ta da kuma binciken ta a kan harkallar kwangiloli na naira bilyan 9.4 a lokacin ta na minista. Hakan bai hana ta zama sanata ba a lokacin, haka kuma bai hana ta sake komawa ba a yanzu.
Duk da binbinin bincike da EFCC ke mata, har yau ba a kai ga gurfanar da ita ba tukunna.
IKE EKWEREMADU
Ike Ekweremadu shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa. Ya sake komawa majalisa ne karo na biyar duk a matsayin mai wakiltar Enugu ta Yamma. Cikin watan Maris, 2018 ne Babbar Kotun Tarayya ta bada umarnin a rike gidajen sa 22 da ya mallaka a Dubai, Abuja, Landan da Amurka, har sai an kammala shari’a da shi tukunna.
EFCC ta tsare shi a cikin Agusta, 2018 aka yi masa tambayoyi, daga bisani aka sake shi.
Har yanzu ana shari’a, kuma ya yi bai ci ko sisi na gwamnati ba.
DANJUMA GOJE
Sanata Danjuma Goje ya yi gwamna a jihar Gombe, tsawon shekaru takwas a karkashin jam’iyyar PDP. Ya koma APC bayan ya zama sanata na Gombe ta Tsakiya. Wannan ne zangon sa na uku zai shiga a majalisar dattawa.
Shekara shida kenan ana tabaka shari’ar taka ruwan cikin Goje da wasu mutane hudu, domin a fitar da naira bilyan 25, amma ko sisi ba a samu ba.
ABDULLAHI ADAMU
Sanata Abdullahi Adamu ya sake komawa kan kujerar sa ta sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta Yamma.
Bayan ya sauka daga gwamnan jihar, an rika bibiyar sa da bincike, har dai a cikin 20110 EFCC ta damke shi, bisa zargin yin rub-da-ciki kan wasu kudi naira bilyan 15 na al’ummar jihar Nasarawa. Shi da wasu mutanen sa 18 ake zargi da yi wa kudaden hadiyar kafino.
Tun da aka maka shi kotu, aka tura shi kurkuku, kuma aka yi belin sa, har yau shekara tara kenan ana tabka shari’a.
Adamu ya koma APC inda ya zama babban gogarman kare Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da ake gurugubjin fada tsakanin Majalisar Dattawa da Fadar Shugaban Kasa.
Cikin Fabrairu, 2018, EFCC ta kuma kama dan sa mai suna Nuraini Adamu, tare da wani mai suna Felix Onyeabo Ojiako, inda ta maka su a Babbar Kotun Jihar Kano, a gaban Mai Shari’a Farouk Lawal.
An zarge su da mallakar wasu kudade ta hanyar shirga karairayi da bayanan dabarar karbar kudaden ba bisa ka’ida ba.
ALIYU WAMAKKO
Wanakko ya sake lashe zaben Sanatan Sokoto ta Arewa. Dama a kan kujerar ya ke, tun bayan saukar sa gwamna.
Ya yi gwamna 2007 zuwa 2011. Sannan kuma ya kara yi a 2011 zuwa 2015. Tun bayan saukar sa gwamna ake tuhumar sa da yi wa naira bilyan 15 hadiyar lomar tuwo.
A cikin 2018 EFCC ta tabbatar da cewa ta na binciken Wamakko a kan cuwa-cuwa da wuru-wurun kudaden jihar Sokoto a lokacin da ya ke gwamna.
Discussion about this post