Sanata Ndume ya koma kan kujerar sa

0

Tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa Ali Ndume na APC ya sake komawa kan kujerar sa ta sanatan Barno ta Kudu.

Kuri’un da aka lissafa ranar Lahadi a Biu, INEC ta tabbatar masa da samun nasara inda Jami’in Bayyana Sakamakon Zabe na INEC, Isa Hassan ya ce Ndume ya samu kuri’u 300, 637, shi kuma dan takarar PDP, Kudla Haske ya samu 84,608.

Yayin da ya ke tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, Ndume ya godewa daukacin jama’ar da ta zabe shi, bisa gagarimin goyon bayan da suka ba shi.

Ya ce ya gode da irin jajircewar da jama’a ta nuna aka fito wurin zabe, duk kuwa da harin da Boko Haram suka kai a garin Pulka.

Ndume shi ne ki wakiltar har da garin Chibok.

Share.

game da Author