A taron samun madafa game da samar da ingantaccen abinci a duniya shugabanin duniya sun amince kan daukan tsauraran matakan da za su taimaka wajen ganin an cimma nasara game da haka.
Taron wanda WHO, AU, FAO da WTO suka shirya ya gudana ne a Addis Ababa babban birnin kasar Ethiopia, ranar Talata.
Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya bayyana cewa samar da abinci mai tsafta da inganci ya zama dole ganin cewa rashin haka na cutar da kiwon lafiyar mutane sannan yana kawo koma bayan tattalin arzikin kasa.
Ghebreyesus ya kara da cewa bincike ya nuna cewa cin abincin da bashi da tsafta da nagarta na cutar da kiwon lafiyar mutane akalla miliyan 600 a duniya wanda daga ciki 420,000 na rasa rayukan su a dalilin haka.
Ya kuma ce binciken ya kara nuna cewa a kasashen da ke tasowa ana asarar akalla dala biliyan 95 duk shekara a dalilin rashin samun abinci mai kyau da nagarta.
Shugaban FOA José Graziano da Silva ya ce samun shugabani dake da kishin kasa, ware isassun kudade sannan yin amfani da kimiya da fasaha wajen inganta aiyukkan noma, ajiye abinci da yadda ake sarrafa abincin na cikin hanyoyin kawar da wannan matsalar.
A karshe taron ya amince da ci gaba da tattauna hanyoyin kawar da wannan matsaloli a duniya gaba daya ranar 23 zuwa 24 ga watan Afrilu a kasar Geneva.
Discussion about this post