Sama da mutane 20,000 ne suka rasa muhallin su a Jihar Kaduna – SEMA

0

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kaduna (SEMA) ta bayyana cewa mutane sama da mutane 20,000 ne suka rasa matsuguni da dukiyoyinsu a jihar Kaduna a shekarar 2018.

SEMA ta fadi haka ne wajen gabatar da rahotannin aiyukkan ta na 2018 ranar Litini a garin Kaduna.

Rahotan ya nuna cewa mutane 20,679 sun zama ‘yan gudun hijira ne a dalilin rikice-rikicen addini, harin ‘yan ta’adda, gobara da ambaliyar ruwa.

‘‘Mutane 20,222 sun rasa gidajen su da dukiyoyinsu a dalilin ambaliyar ruwa, 6457 sun zama ‘yan gudun hijira a dalilin aiyukkan mahara.

” Jihar ta rasa rayukan mutane 256 a dalilin aiyukkan mahara da rikice-rikice, mutane 150 sun sami rauni a jikkunan su sannan 11 sun bace a dalilin aiyukkan mahara da rikicin addini.

Rahotan ya nuna cewa ambaliyar ruwa ta tafi da gidaje da gonaki 12,454 da asarar ya kai har Naira biliyan 4.6.

” Ambaliyar ruwa ta shafi kauyuka 60 a kananan hukumomi 14 a jihar.”

Duk a cikin rahoton, gobara ta babbake gidaje 58, dakunan kwanan dalibai 150 da kauyukan 10 sannan an kona gidaje 150 da shaguna 300 a dalilin rikice-rikice da aka yi fama dashi a Jihar.

Wani bene mai hawa biyu ta rushe sannan iskar ruwa ya yaye jinkan gidaje 250.

Share.

game da Author