SAMA DA FADI: ICPC ta kama shugaban Hukumar mazu ziyarar Bauta, Jarusalem

0

Hukumar ICPC ta kama shugaban hukumar kula da masu ziyarar bauta a kasar Jarusalem (CPWB) Jinga Mayo bisa zargin sama da fadi da yayi da kudaden hukumar.

Kakakin hukumar ICPC Rasheedat Okoduwa ta sanar da haka a wata takardar da ta raba wa manema labarai ranar Talata.

Rasheedat ta bayyana cewa ana tuhumar Mayo ya yi sama da fadi da Naira miliyan 69.2 wanda aka ware domin biyan ma’aikatan hukumar na jihar Adamawa.

” Muna kuma tuhumarsa da saka hannu a wasu takardu da suka nuna an karba kuma an biya wadannan ma’aikata alhalin shi Mayo bai biya ma’aikatan ba.

A yanzu dai an gurfana da Mayo a gaban alkalin babbar kotun dake Yola, Nathan Musa.

Mayo bai amince ya aikata wannan laifi ba.

Shi kuwa lauyan da ya shigar da karar, Mohammed Kolo ya nemi kotu da ta tsayar da ranar sauraron shari’ar.

Alkali Musa ya bada belin Mayo akan Naira miliyan 30, da gabatar da shaida daya dake zama a inda kotu dake da iko da wurin.

Share.

game da Author