SAKAMAKON ZABE: Atiku ya garzaya kotu da tulin hujjojin zargin magudi

0

Dan takarar shugaban kasa na jama’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa wanda INEC ta bayyana a yau da asubahin ranar Laraba.

INEC ta sanar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari na APC ya samu kuri’u 15,191,847, shi kuma Atiku ya samu 11,262,978.

Amma kuma jim kadan bayan bayyana cewa Buhari ne ya yi nasara, Atiku ya fitar da kakkausan kalamin rashin amincewa da zakamakon zaben.
Ya kuma kawo hujjojin da ya ke ganin cewa an tabka magudi a karkashin jawabin da ya fitar a safiyar yau Laraba.

Akwai tulin hijjoji na bidiyo inda aka rika nuno yadda aka yi magudi a zaben na 2019 na shugaban kasa fa aka gabatar ranar Asabar da ta wuce.

” Idan da a ce an kayar da ni a zabe na gaskiya da gaskiya, to da tuni na kira wanda yayi nasara ta taya shi murna. Kuma da na taya shi aikin dinke barakar da ke tsakanin Arewaci da Kudancin kasar nan.”Inji Atiku.

” Amma tsawo shekaru kusan talatin na dawowar dimokradiyya a kasar nan, ban taba ganin zaben da aka ci mutuncin dimokradiyya kamar zaben ranar 23 Ga Fabrairu, 2019 ba.

Atiku ya ce bai yarda da sakamakon zaben ba, kuma ya na kira ga magoya bayan sa cewa ba zai amince da sakamakon ba har ya bada kai bori ya hau.

Atiku ya kuma gode wa miliyoyin ‘yan Najeriya da suka fito suka jefa kuri’a.

Wannan ya na nufin Atiku zai garzaya kotu kenan.

Atiku ya ci gaba da bayar da dimbin misalai da dama a inda ya ce an yi kwacen akwatinan zabe, magudi, murdiyya, danniya, aringizo, cin zarafin masu adawa da tauye musu hakkin zabe musamman da ya ce sojoji sun yi.

Ya yawaita misalai daga abubuwan da suka faru a jihohin Legas, Akwa Ibom da Ribas da wasu jihohi.

Cikin bidiyo guda 16 da Kakakin Yada Labaran Atiku, ya turo wa PREMIUM TIMES,

Akwai bidiyon da ke nuna rikici, akwai wadanda ke nuna inda masu bindigogi ke tarwatsa masu zabe ko masu kidaya kuri’u, akwai kuma inda ake aringizon kuri’u da kuma kekketa kuri’un da aka jefa.

Gaba daya dai bidiyo 16 ne masu nuna tashe-tashen hankula a jihohi musamman Legas, Ribas da Akwa Ibom inda Atiku ya nuna cewa duk rikice-rikicen sun tashi ne a inda PDP ke da rinjayen masu zabe ko kuma rinjayen kuri’u.

Share.

game da Author