Hukumar Hana Sha da Safarar Muggan Kwayoyi (NDLEA), ta bayyana wani babban kamu da ta yi na masu ta’ammali da muggan kwayoyi a Jihar Kano.
Kwamandan Hukumar na Jihar Kano, Ibrahim Abdul, ya bayyana wa manema labarai a yau Litinin cewa sun tarwatsa majalisar shan kwayoyi har wurare 35 a cikin unguwanni daban-daban.
Unguwannin da aka tarwatsa kuma aka damke ‘yan kwayar, sun hada da: Bakin Plaza a Fagge, Sanya Olu a cikin Sabongari, Kabuga, Rimin Kebe, kauyen Danzaki da kuma Sauna.
Sauran wuraren sun hada da: Warure, Aisami, Sabon Titi, Dorayi, Hauren Gadagi, Kwanar Danmarke, Challawa, Madobi, Ring Road, Farawa, Mariri, Farin Ruwa da sauran su.
Kwamandan ya kara shaida wa manema labarai cewa an yi wannan gagarimin kamen ne a cikin wata daya da ya gabata.
Ya kara da cewa za a ci gaba da rarakar mashaya kwayar har sai an fatattake su gaba daya.
Abdul ya ce an samu nasarar damke wani dan kabilar Igbo mai suna Okechukwu Echefu, wanda aka kama da katan 9 jabun kwayoyin maganin Coartem, katan 7 na kwayar jabun maganin Augmentine da kuma katan biyu na Laclox shi ma jabu, sai kuma katan biyu na wasu tarkacen jabun magunguna.
Dangane da kamu kuwa, ya ce an kama mashaya kwaya 176, amma takwas daga cikin su mata ne.
An kuma binciki cewa Okechukwu ya na shigo da magungunan na jabu ne daga kasashen waje.
An jima samu wata kwaya da ake kira ‘Khat’ da ake shigo da ita daga Afrika ta Kudu, duk a hannun sa.
Kwamandan ya ce za a tura shi a hannun shari’a da an bincike.
Ya yi kiran gwamnati da sarakunan gargaiya su kara kaimi wajen ja wa al’umma, musamman matasa kunne.